Magidanci Ya Yi Wa Matarsa Yankan Rago Saboda Jinkiri Wajen Hada Masa Shayi

Magidanci Ya Yi Wa Matarsa Yankan Rago Saboda Jinkiri Wajen Hada Masa Shayi

  • Wani mutumin kasar Indiya mai suna Dharamveer ya fille kan matarsa, Sundari, sakamakon tunzura da ya yi saboda ta yi jinkiri wajen kawo masa shayin safe a Ghaziabad, kusa da Delhi
  • An rahoto cewa Dharamveer, mai shekaru 52 ya caki matarsa da takobi sau 15 kafin ya aikata mugun aikin
  • Dalilinsa na aikata wannan mummunan aika-aikar shine cewa Sundari ta dade wajen hada masa shayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Delhi, India - Wani magidanci ya caki matarsa sau 15 kafin ya fille mata kai da takobi a kauyen Faljagadh, Uttar Pradesh, Delhi.

Kamar yadda Daily Mail ta rahoto, fusataccen mijin mai suna Dharamveer ya kashe matarsa, Sundari a wani irin yanayi na rashin imani kan ta yi jinkirin hada masa shayin safe a ranar Talata, 19 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yi murabus daga gwamnatin Tinubu, Lalong ya magantu

Magidanci ya kashe matarsa saboda shayi
Magidanci Ya Fille Kan Matarsa Saboda Jinkiri Wajen Kawo Masa Shayi Hoto: Le Club Symphonie
Asali: Getty Images

Magidanci ya kashe matarsa da takobi

A cewar Times of India, dattijon mai shekaru 52 ya tashi yan mintuna bayan matarsa mai shekaru 50, wacce tuni ta fara hada masa shayin, kuma nan take ya tambayi ina yake.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar yan sanda ta ce yayin da matar ta bukaci mijin ya bata mintuna 10 ta kammala shirya masa shayin, sai Dharamveer ya fusata sannan ya gaggauta daukar makamin wanda ya yi amfani da shi wajen halaka matar tasa a kicin.

Jami'in dan sanda, Vivek Yadav ya bayyana cewa Sundari ta tashi tun karfe 6:00 na asubahi domin hada shayin kamar yadda ta saba duk safe.

Danna nan don ganin hotunan mutumin da matarsa.

Kamar yadda rundunar yan sandan ta bayyana, yaran ma'uratan hudu suna bacci lokacin da mummunan al'amarin ya afku.

Kara karanta wannan

Direban tasi ya tsinci jakar kudi a motarsa, bidiyo ya bayyana yayin da ya mayar da shi

Yadav ya ce:

"Bayan kamar mintuna biyar, Dharamveer ya sake tambayar ina shayin sannan ya gaggauta shiga kicin din. Ya fusata lokacin da matar ta fada masa cewa zai dauki kamar mintuna 10 kafin ya shayin ya kammalu sai ya buge kayan kicin din.
"Sai ya je ya dauko takobi kafin ya koma ya yi amfani da shi wajen kashe matar tasa."

Lokacin da dansu mai suna Soldier, ya ji karar matar, sai ya gaggauta zuwa wajen, inda ya tarar da mahaifiyarsa cikin jini.

An kuma rahoto cewa Dharamveer ya farmaki yaran a lokacin da suke kokarin taimaka mata, sai suka tsere guda dakinsu.

Soldier ya tuna:

"Ni da kannena mata biyu mun yi kokarin ceton mahaifiyarmu, amma mahaifinmu ya yi barazanar kashe mu. Wannan ne dalilin da yasa muka bar wajen. Mahaifina Dharamvir yayin da yake tserewa ta wajen rake da aka shuka yana ta wurga takobin saboda kada wanda ya kama shi."

Kara karanta wannan

To fah: Fitaccen malami ya ayyana shiga tseren takarar gwamna a jihar PDP, ya faɗi dalili

Mutanen kauyen sun ruga zuwa gidan sakamakon jin kukan yaran inda suka tarar da gawar Sundari a kwance cikin jini.

Sun kira yan sanda sannan aka dauke gawar Sundari.

Soldier ya sanar da kafar labaran Indiya cewa mahaifinsu ya sha fusata a baya saboda shayi kuma ya kan yi wa mahaifiyarsu ihu, amma bai taba dukanta ba.

Magidanci ya kashe matarsa saboda abinci

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa jami'an yan sanda sun kama wani magidanci kan zargin kashe matarsa saboda ta ki girka abincin da ya fi so a yankin Olota da ke karamar hukumar Alimosho ta jihar Lagas.

Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, lokacin da mijin ya dawo daga wajen aiki sannan ya ga cewa matar ta girka taliya ne ba abincin da ya fi so ba, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng