Harin Sojojin Najeriya Kan Farar Hula: Miyetti Allah Ta Kafa Wa Tinubu Wani Muhimmin Sharadi

Harin Sojojin Najeriya Kan Farar Hula: Miyetti Allah Ta Kafa Wa Tinubu Wani Muhimmin Sharadi

  • An yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta gaggauta biyan diyyar farar hula da sojojin Najeriya suka kashe a hare-haren sama a fadin kasar
  • Kungiyar Miyetti Allah ta kasa ce ta yi wannan kiran inda shugabanta, Othman-Ngelzarma ya ce akwai bukatar a waiwayi makiyayan da aka kashe a Rukubi
  • Othman-Ngelzarma ya ce kungiyar ta sa ido ta ga ko kungiyar gwamnoni, 'yan majalisun tarayya za su cika alkawuran da suka dauka a Tudun Biri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta nemi gwamnatin Tinubu ta diyyar farar hular da sojoji suka kashe a harin bama-bamai a fadin kasar.

Shugaban kungiyar MACBAN na kasa, Baba Othman-Ngelzarma, ya gabatar da bukatar a ranar Laraba a Abuja, inda ya roki sojoji su rinka yin taka tsan-tsan yayin kai harin sama.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Miyetti Allah na son Tinubu ya biya diyyar kisan farar hula a Najeriya
Kungiyar Miyetti Allah ta nemi Tinubu ya biya diyyar farar hular da sojoji suka kashe a harin bama-bamai a fadin kasar. Hoto: MACBAN
Asali: Facebook

Matsayar Miyetti Allah kan kisan makiyaya a Rukuba

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa an bi kadin wasu 'yan ba ruwana da aka kashe a Rukubi, gundumar Doma, jihar Nasarawa a ranar 27 ga watan Janairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sa, mutanen sun mutu ne sakamakon wani harin bam da sojojin saman Najeriya suka kai masu, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce:

"Makiyaya ne da ke tafiya da dabbobinsu bayan biyan gwamnatin Benue naira miliyan 29 kan dabbobin. Ya zama wajibi a bi kadin jininsu da sojoji suka zubar."

Vanguard ta ruwaito Othman-Ngelzarma na cewa irin wannan harin ya faru a Tudun Biri a jihar Kaduna, wanda a ganinsa ba gwamnati kadai ba, har sojoji ya kamata su biya diyyar wadanda aka kashe.

Rokon Miyetti Allah ga gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Ya kara da cewa:

"Mun ga yadda kungiyar gwamnonin Arewa da 'yan majalisun tarayya da wasu hukumomin kasar sun ziyarci Tudun Biri, sun yi alkawurra, to muna jira a cika su.
"Muna kira ga gwamnati ta biya diyyar mutanen da aka kashe a Rukubi kamar yadda za a biya na Tudun Biri, su ma 'yan Najeriya ne kamar kowa."

A karshe shugaban kungiyar Miyetti Allah ya ce zuwa yanzu ya kamata gwamnatin Tinubu ta fito ta fadi adadin kudin da za ta biya iyalan da aka kashe 'yan uwansu a hare-haren soji a kasar.

Yan bindiga sun kashe malamin kwalejin ilimi ta Zamfara

A wani labarin, 'yan bindiga sun kashe malamin kwalejin ilimi ta jihar Zamfara bayan makonni uku da yin garkuwa da shi tare da wasu da dama.

Yan bindigar sun kashe Malam Nasiru Mohammed Anka bayan karbar kudin fansa har naira miliyan biyu daga iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.