Dakarun Sojoji Sun Sheke Dan Bindiga Sun Kwato Muggan Makamai a Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Sheke Dan Bindiga Sun Kwato Muggan Makamai a Kaduna

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri na ƴan bindiga masu tayar da ƙayar baya a jihar Kaduna
  • Dakarun sojojin sun halaka wani ɗan bindiga ɗaya a Sabon Birni cikin ƙaramar hukumar Igabi ta jihar a wani kwanton ɓauna
  • Hakazalika dakarun sun raunata ƴan bindiga da dama tare da ƙwato muggan makamai da alburusai a hannun miyagun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya ta ɗaya a ranar Laraba ta ce dakarunta sun kashe wani ɗan bindiga tare da ƙwato makamai da alburusai a Sabon Birni da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

A cewar sanarwar da muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanal Kanal Musa Yahaya ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 17 ga watan Disamba, lokacin da sojoji suka yi wa wasu ƴan bindiga kwanton ɓauna a yankin.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta kasa ta yi wa Shugaba Tinubu da CBN babbar barazana kan abu 1 tak

Dakarun sojoji sun halaka dan bindiga
Dakarun sojoji sun salwantar da ran dan bindiga a Kaduna Hoto: @NigerianArmy
Asali: Twitter

Ya ce sojojin sun kwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da wata jigida ɗauke da alburusai 15 masu kaurin 7.62mm, rediyon Baofeng da wayoyi guda biyu, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika rundunar sojojin a wani samame da suka kai a hanyar Dende-Buruku a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna a ranar 15 ga watan Disamba, sun yi wa wasu ƴan bindiga kwantan ɓauna, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Sojojin sun ƙwato makamai masu tarin yawa

"A yayin farmakin, ƴan bindiga da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da sojoji suka kwato bindiga kirar AK-47 da kuma wata jigida ta bindigar AK-47 ɗauke da alburusai guda huɗu masu kaurin 7.6mm." A cewarsa.

Yahaya ya ce babban jami’in rundunar, wanda kuma shi ne kwamandan rundunar ‘Operation WHIRL PUNCH’, Manjo Janar Valentine Okoro, ya yabawa sojojin bisa jajircewar da suka yi.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin yan siyasan da suka sanya hannu a yarjejeniya kawo karshen rikicin Rivers

Ya buƙace su da su cigaba da hana ƴan bindiga, ƴan ta'adda da duk wasu ɓata gari ƴancin gudanar da ayyukansu.

Sojoji Sun Halaka Ƴan Ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar sheƙe wasu miyagun ƴan ta'adda mutum uku a jihar Sokoto.

Dakarun sojojin sun kuma yi nasarar ceto wasu mutum shida da ƴan ta'addan suka sace a wani ƙazamin artabu da suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng