An Shiga Dar-Dar Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Mace Mai Juna Biyu, Da Wasu Mutum 22 a Taraba
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da sace wasu jami'anta guda biyu, mace mai ciki, da wasu mutum 21 a jihar Taraba
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun farmaki garin Pupule da ke karamar hukumar Yaro, inda suka yi harbi kan mai uwa da wabi
- Tuni dai rundunar 'yan sandan ta tura dakarunta na sashen kai farmaki da na sashen yaki da masu garkuwa don ceto wadanda aka kama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Taraba - Al'ummar garin Pupule a karamar hukumar Yoro, jihar Taraba sun shiga tashin hankali yayi da 'yan bindiga suka sace mace mai juna biyu, basarake, 'yan sanda biyu da wasu mutum 21.
Wani da abin ya faru gabansa ya shaida cewa 'yan bindigar sun mamaye garin Pupule a safiyar ranar Talata haye kan babura kuma dauke da muggan makamai.
Yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, inda suka dasa tsoro a zukatan mazauna garin wanda ya basu damar yi masu dauka dai-dai daga gidajensu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan bindigar suka kai hari da matakin da 'yan sanda suka dauka
A cewar wani Mr Tundu Ibahem, mzaunin garin, 'yan bindiga sun cuna wa basaraken da dansa bindiga, inda suka yi awon gaba da su.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun tafi da wata mata mai dauke da juna biyu tare da wasu da dama daga iyalanta.
Sai dai a cewar Ibahem har yanzu 'yan bindigar basu kira waya don fadin bukatunsu ba, inda ya ke cewa:
"Kowa na kwance a dakinsa lokacin da 'yan bindigar suka mamaye garin a tsakiyar dare, suka yi harbi sosai, hakan ya tsoratar da mutane, babu wanda ya iya yin komai."
The Guardian ta ruwaito Abdullahi Usman, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba ya na bayyana cewa 'yan sandan biyu da aka sace sufeto ne da mai mukamin sajen.
Usman ya bayar da tabbacin cewa rundunar ta rarraba jami'anta na sashen kai farmaki da sashen dakile masu garkuwa da mutane, inda ya ke fatan kwato wadanda aka sace tare da kamo masu laifin.
Sufetan 'yan sanda ya bindige kansa bayan harbe abokin aikinsa a Rivers
A wani labarin, wani Sufeto a rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ya kashe kansa bayan da aka ce ya harbe abokin aikinsa Monday Gbaramana har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa dan sandan mai suna Sufeto Nelson Abuante ya harbe abokin aikinsa a ranar Lahadi a Nyogor-Lueku da ke karamar hukumar Khana a jihar.
Asali: Legit.ng