Karshen Shekara: Manyan Abubuwa 7 da Suka Faru a 2023 da Suka Canja Siyasar Najeriya

Karshen Shekara: Manyan Abubuwa 7 da Suka Faru a 2023 da Suka Canja Siyasar Najeriya

  • Shekarar 2023 na daf da zuwa karshe, kuma abubuwa da dama sun faru da ya canja salon siyasar Najeriya, kama daga tashin hankali zuwa farin ciki
  • Daga babban zaben 2023 da ya samar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma rikicin siyasa a wasu jihohi, siyasar kasar ta zama abar kallo a duniya
  • A wannan gabar, jaridar Legit ta yi waiwaye kan wasu muhimman abubuwa da suka faru a 2023 da ya canja siyasar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - An samu gagarumin canji a siyasar Najeriya tun bayan kammala zaben 2023, abubuwa da dama sun faru kama daga abubuwan farin ciki da na tashin hankali.

A wannan wallafar, Legit Hausa ta yi fashin baki kan siyasar Najeriya a 2023, inda za mu yi nazarin manyan abubuwan da suka kawo babban sauyi a mulki da rayuwar 'yan kasar.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun fusata yayin da shugaba Tinubu ya umarci gwamnan PDP ya canza kasafin 2024

Manyan abubuwa 7 da suka faru a siyasar Najeriya a 2023
Daga rikicin siyasar Kano, Rivers da dambarwar takardun Tinubu, Legit ta lissafa abubuwa 7 da suka shiga tarihin siyasar Najeriya a 2023. Hoto: @officialABAT, @Kyusufabba, @GovWike
Asali: Twitter

Da farko bari mu fara yin nazari wasu manyan abubuwa bakwai da suka faru, wadanda za su zamar mana matashiya kan auna ci gaba da koma baya da aka samu a dimokuradiyyar kasar.

1. Wike as FCT minister

Siyasar Najeriya ba za ta taba mantawa da nadin Nyesom Wike matsayin ministan Abuja a gwamnatin Tinubu ba, musamman kasancewarsa dan hamayya daga jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma babu wanda zai iya karyata irin gwagwarmayar da Wike ya yi har Tinubu ya samu nasara a jihar Rivers, bayan shan suka da tsangwama daga jagororin PDP.

Wike ya zama dan shiyyar Kudu na farko da ya zama ministan Abuja tun bayan kafa dimokuradiyya a 1999, dukkan wadanda suka rike mukamin sun fito daga shiyyar Arewa.

2. Rantsar da Tinubu/Cire tallafin man fetur

Tinubu ya yi kaurin suna tun bayan da aka rantsar da shi matsayin shugaban Najeriya na 16, bayan da ya janye tallafin man fetur, lamarin da ya jefa kasar cikin mugun yanayi.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Janye tallafin man fetur ya haddasa hauhawar farashin man fetur din kansa, inda kayayyakin abinci da na masarufi suka yi tashin gwauron zabi, rayuwa ta yi tsada a cikin kasar.

3. Rikicin Rivers (Wike Vs Fubara)

Babban labarin da ya yi kaurin suna a Najeriya shi ne rikicin siyasa tsakanin tsohon gwamnan Rivers Wike da magajinsa Fubara, har kawo yanzu ba a ga maciji tsakanin yan siyasar biyu.

Wutar rikicin ta kara ruruwa bayan wani abun fashewa ya fashe a ginin majalisar jihar a wani yunkuri da aka yi na tsige Fubara daga gwamnan jihar, amma ya fito ya ba da hakuri.

4. Rikicin jihar Edo (Obaseki Vs Shaibu)

Rikici tsakanin gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da mataimakinsa Philip Shaibu ya ja hankali, inda Shaibu ya fito ya nuna sha'awarsa na tsayawa takarar gwamnan jihar.

An fara takun sakar tsakanin gwamnan da mataimakinsa bayan da Obaseki ya zargi Shaibu da yunkurin yi masa juyin mulki da kuma yi wa gwamnatinsa zagon kasa.

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

5. Rikicin jihar Kano (Abba Vs Gawuna)

Tun bayan kammala zaben 2023, siyasar jihar Kano ta dauki zafi bayan da jam'iyyar NNPP ta kawo kujerar gwamna, abin da ya ke shirin juyewa a kotu bayan da aka soke zaben Gwamna Yusuf.

Kotun karar zabe da Kotun Daukaka Kara duk sun kori Yusuf tare da ayyana Nasir Gawuna matsayin gwamna, lamarin da ya jawo tashin tashina a jihar na dogon lokaci, tuni Abba ya garzaya Kotun Koli.

5. Dambarwar takardun makarantar Tinubu na CSU

An tafka babbar muhawara kan ingancin takardun makarantar Tinubu na jami'ar jihar Chicago, Atiku ya mika wa kotun Amurka bukatar son mallakar takardun makarantar shugaban kasar.

Wannan bambarwar ta kai ga taba martabar dimokuradiyyar Najeriya, inda Tinubu ya yi iya kokarinsa na kare zargin da Atiku ke masa na amfani da takardun makaranta na bogi, a karshe kotu ta kori karar da Atiku ya shigar.

Kara karanta wannan

A Karshe, Shugaba Tinubu ya sansanta rikicin minista da gwamnan PDP kan sharuɗda 8

6. Peter Obi da masu hankoron kare muradunsa

Dan hakin da Tinubu da Atiku suka raina, wato Peter Obi ya zo ya zamar masu ala kai-kai a zaben 2023 bayan da ya mamaye jihohi 12, ciki har da Legas da Abuja.

Duk da cewa Obi bai zama na biyu a zaben shugaban kasa ba, sai dai jam'iyyarsa ta LP ta kawo 'yan majalisun jihohi da tarayya har ma da kujerar gwamna, lamarin da ya ja hankali a siyasar kasar.

Simon Lalong ya ajiye mukamin minista da Tinubu ya ba shi

A wani labarin, Sanata Simon Lalong ya ajiye mukamin ministan kwadago da samar da ayyuka a gwamnatin Tinubu domin karbar kujerar Sanatan Filato ta Kudu a majalisar dattijai.

Tuni dai shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da wannan murabus din, inda ya yi masa fatan alkairi a sabon aikin da zai fara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.