“Larabci Harshe Ne da Ba Na Biyunsa”, Zulum Zai Gina Makarantun Islama Guda 27 a Borno

“Larabci Harshe Ne da Ba Na Biyunsa”, Zulum Zai Gina Makarantun Islama Guda 27 a Borno

  • Gwamnatin jihar Borno ta sha alwashin kammala gina makarantun koyon addini da Larabci guda 27 a fadin jihar kafin saukar Gwamna Zulum
  • Mai girma gwamna Zulum ne ya sha alwashin a taron tunawa da ranar Larabci ta duniya karo na 18 a Maiduguri
  • Zulum ya ce ya zuwa yanzu ya kafa makarantun Larabci guda takwas, kuma yana sa zan kammala sauran don bunkasa harshen da addini

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bada tabbacin kammala kwalejojin Islama guda 27 domin inganta karatun Larabci da na addinin musulunci a fadin jihar.

A taron tunawa da ranar Larabci ta duniya karo na 18 a Maiduguri, gwamnan ya ce zai ci gaba da bayar da goyon baya wajen inganta wa da yada harshen Larabci a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

A karshe: Simon Lalong ya ajiye mukamin minista da Tinubu ya bashi, an samu cikakkun bayani

Zulum zai gina kwaleji 27 na koyon Larabci a Borno
Zulum ya bada tabbacin kammala kwalejojin Islama guda 27 don inganta karatun Larabci da na Islama a fadin jihar. Hoto: @ProfZulum
Asali: Twitter

Wanne kokari Zulum ya yi don samar da makarantun?

Zulum ya ce Larabci harshe ne da babu na biyun sa a harsunan duniyar nan, don haka dole ne gwamnatinsa ta tabbatar da habaka wa da yada shi, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Jihar Borno ta yi alkawarin samar da kwalejojin Larabci guda 27, inda yanzu muka kafa kusan guda takwas, kuma insha Allahu kafin cikar wa’adina za mu kaddamar da dukkan su."

Farfesa Muhammad Umaru Ndagi na sashen nazarin harsuna a jami’ar Abuja, ya yi kira ga mahalarta taron da su rika kallon Larabci matsayin cikakken harshe ko ba don addini ba.

Ya ce Larabci ya taba zama harshen kimiyya da fasaha a duniya.

Yan bindiga sun kashe malamin kwalejin ilimi ta Zamfara

A wani labarin, Malam Nasiru Mohammed Anka, malami a kwalejin ilimi ta jihar Zamfara da ke Maru ya gamu da ajalinsa a hannun wasu 'yan bindiga bayan karbar kudin fansa har naira miliyan biyu.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

An yi garkuwa da marigayi Malam Mohammed ne a gidansa, wani rukunin gidajen gwamnati da ke kusa da kwalejin a Maru kimanin makonni uku da suka gabata.

Yan bindigar sun yi garkuwa da shi ne tare da wasu mazauna unguwar lokacin da suka mamaye rukunin gidajen tare da daukar mutane da dama domin neman kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.