‘Dan Majalisar NNPP Ya Kuma Taimakawa Mata 500 da Kudi a Mazabarsa a Jihar Kano
- Abdulmumin Jibrin ya sake yin rabon tsabar kudi ga al’ummar da yake wakilta a majalisar wakilan tarayya
- ‘Dan majalisar na Kano ya tallafawa mata 500 a wannan karo, an zabo matan ne daga mahaifarsa ta Kofa
- Kafin yanzu, Hon. Abdulmumin Jibrin ya taimakawa mutane da-dama da kudi a yankunan Kiriu da Bebeji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Abdulmumin Jibrin mai wakiltar Kiru da Bebeji a majalisar wakilai ya cigaba da tallafawa mutanen mazabarsa.
‘Dan majalisar tarayyan ya shaida haka a shafinsa na Twitter, ya ce ya rabawa mata har 500 kudi a tsare-tsaren tallafinsa.
Tallafin Abdulmumin Jibrin a Majalisa
A bayanin da ya yi, ya bada tallafin ne a ranar Lahadi, wanda wannan shi ne karo na bakwai da ya yi irinsa a majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Abdulmumin Jibrin wanda aka rantsar a watan Yuni ya nuna ba wannan ne karon farko da ya bada tallafi ba.
Da yake magana a dandalin na Twitter, ‘dan majalisar mai wakiltar Kiru da Bebeji ya ce sau bakwai yana bada tallafi.
A cewar ‘dan majalisar na jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano, maza da mata sun amfana da tsarin tallafinsa a majalisa.
Siyasar Kano da shari'ar NNPP v APC
An yi rabon ne kwana biyu bayan Hon. Jibrin ya hadu da Bola Tinubu a Aso Rock.
Dalilin zamansa da shugaban kasa shi ne yadda za a shawo kan matsalar siyasar Kano inda za ayi shari'a a kotun koli.
Jawabin Abdulmumin Jibrin (NNPP)
“HON ABDULMUMIN JIBRIN YA SAKE TALLAFAWA MATA 500 DA KUDI
A cigaban tsare-tsaren tallafinsa ga mutanen mazabarsa, A ranar Lahadi, Hon. Jibrin ya sake tallafawa mata 500 da tsabar kudi 500.
Wannan ne karo na bakwai da aka bada tallafi kuma karo na biyu da aka yi wa mata.
Nade-naden Abba Gida Gida
Daga jihar ta Kano, ana da labari Gwamna Abba Kabir Yusuf yana cigaba da yin ruwan nade-naden mukamai har gobe.
Wannan karo Gwamna ya shiga kowace karamar hukuma da ake da ita, ya aika mata wasu jami’ai da abin ya jawo surutu.
Wasu suna ganin an yi nadin wadannan jami’ai ne saboda wofantar da shugabannin kananan hukumomi da ‘Yan APC ne.
Asali: Legit.ng