Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka ‘Sace’ Mawaki da Masu Ƴan Amshinsa a Abuja
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace wani mawaki da masu masa kida a hanyar Abuja zuwa Kogi
- Wani mawaki Boye Best ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram inda ya ce 'yan bindigar suna neman naira miliyan 10 kudin fansar duk mutum daya
- Boye Best ya koka kan yadda Najeriya ta koma kan matsalar tsaro tare da rokon jama'a su kai masu dauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An shiga firgici a safiyar Litinin kan rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani mawakin Juju dan Najeriya, Omoba De Jombo Beats tare da masu masa kida a ranar Lahadi.
Rahotannin da ke yawo a yanar gizo na cewa, mawakin da ‘yan tawagarsa na dawowa daga wani taro lokacin da aka yi garkuwa da su.
An kama wani mutum bayan ya ziyarci surukansa ba tare da sadaki ba, sun dafa abinci da komai na biki
Wani mawaki da aka fi sani da Boyebest, ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram inda ya koka kan wannan lamari da ya faru a karshen makon da ya gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudin da 'yan bindigar suke nema - Boye Best
Boye Best ya yi wa labarin nasa taken, “An yi garkuwa da mawaki da dukkan tawagar makadansa. Lallai Najeriya ta lalace."
An gano cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da su bayan sun yi wani wasa a Abuja a karshen mako, cewar Vanguard.
Boye Best ya ce:
"An yi garkuwa da Omoba De Jombo Beats da makadansa a hanyarsu ta zuwa Kogi daga Abuja bayan yin wasa a ranar Lahadi.
"Muna neman taimakon ju jama'a saboda masu garkuwan na neman naira miliyan 10 kudin fansa kan kowanne mutum daya."
Shugaban majalisar dattawa ya yi magana kan rade-radin ya yanke jiki ya fadi a bikin cika shekaru 61
A karshe Boye Best ya yi wa mawakin da masu masa kida addu'ar fita daga hannun masu garkuwa da mutanen lami lafiya.
Ga abin da ya wallafa:
Yan bindiga sun mamaye garin Zurmi, jihar Zamfara
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito yadda mazauna garin Zurmi da ke jihar Zamfara suka koka tare da neman agaji kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kai wa kauyen hare-hare.
A makon da ya gabata, 'yan bindiga sun farmaki garin har sau hudu, inda suka kashe mutum uku da sace wasu 16, tare da kona ofishin ‘yan sanda da motocin aikin soja guda biyu.
Asali: Legit.ng