Abin Bai Yi Dadi Ba: ’Yan Bindiga Sun Mamaye Wani Gari a Zamfara, Sun Kashe Mutune
- Yan bindiga sun kai wasu sabbin hare-hare a garin Zurmi da ke jihar Zamfara, inda suka kashe akalla mutum uku tare da yin garkuwa da wasu
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar na kai hare-haren ne biyo bayan kwace shanun sata da sojoji suka yi daga hannun su
- Tuni dai wasu daga cikin mazauna garin suka fara yin hijira don tsira da rayukansu daga hare-haren 'yan bindigar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zurmi, jihar Zamfara - Al’ummar garin Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara sun koka tare da neman agajin kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kai wa kauyen hare-hare.
A makon da ya gabata, 'yan bindiga sun farmaki garin har sau hudu, inda suka kashe mutum uku da sace wasu 16, tare da kona ofishin ‘yan sanda da motocin aikin soja guda biyu.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa wasu fitattun jagororin ‘yan fashi guda biyu, Sani Black da Sani Dan Karami ne suka jagoranci hare-haren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa 'yan bindiga ke kai hari garin Zurmi?
Wani mazaunin garin Auwalu Musa ya ce ‘yan bindigar sun sake komawa kauyen jiya inda suka yi garkuwa da wasu mata hudu.
Wani mazaunin garin Malam Aliyu Zurmi (ba sunansa na gaskiya ba) ya ce ‘yan bindigar na kai wa garin hari ne saboda sojoji sun kwato musu dabbobin da suka sace a wani lokaci da ya wuce.
Zurmi ya ce sojoji sun kwato dabbobin daga hannun Sani Black, inda shi kuma ya kai masu hari a ranar Asabar da Litinin don daukar fansa.
Halin da mazauna Zurmi ke shiga a hare-haren 'yan bindiga
Mallam Musa Bello ya ce yana gida lokacin da 'yan bindiga suka kai hari garin ranar Litinin, amma sojoji sun kai masa dauki yayin da 'yan bindigar ke kokarin balla kofar gidansa.
Wani mazaunin garin, Alhaji Sulaiman Ibrahim, ya ce akwai ban tsoro harin da 'yan bindigar ke masu, inda ya tariyo yadda sojoji suka yi ba ta kashi da 'yan bindigar tsawon wa biyu.
Wani magidanci, Zurmi ya ce a yanzu dai an samu kwanciyar hankali amma tuni ya yi hijira daga garin har sai komai ya lafa sannan ya koma.
Simon Lalong ya ajiye mukamin minista a gwamnatin Tinubu
A wani labarin, Simon Lalong ya bar majalisar ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a hukumance domin ya karbi kujerar sa ta majalisar dattawa.
Tsohon gwamnan Filato ya mika takardar yin murabus a makon da ya gabata, kuma shugaba Tinubu ya amince da hakan, rahoton Legit Hasua.
Asali: Legit.ng