Masana Sun Yi Sharhi Kan Tsadar Simintin BUA Bayan Alkawarin Buhu Zai Sauka Zuwa N3,500

Masana Sun Yi Sharhi Kan Tsadar Simintin BUA Bayan Alkawarin Buhu Zai Sauka Zuwa N3,500

  • Ana ci gaba da siyar da simintin BUA sama da N5,000 duk da sanar da rage farashinsa da kamfanin ya yi a baya
  • Manazarta dai sun danganta hakan da tsadar kudin da ake kashewa wajen safarar kayayyaki sakamakon cire tallafin man fetur
  • Wannan na zuwa ne daidai da binciken da aka yi a jihohin Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Biyo bayan sanar da rage farashin simintin BUA zuwa N3,500 a watan Oktoba, gar yanzu farashinsa bai sauya daga yadda yake a kasuwanni kafin sanarwar ba.

Idan baku manta ba, rahotonmu na baya ya naqalto yadda kamfanin ya sanar da ragin tare da fadin dalilinsa na yin haka.

Kara karanta wannan

An kama wani mutum bayan ya ziyarci surukansa ba tare da sadaki ba, sun dafa abinci da komai na biki

Dalilin tsadar simintin BUA
Ana siyar da simintin BUA da tsada har yanzu | Hoto: Bua Cement
Asali: UGC

Simintin mai nauyin 50kg ana siyar dashi a farashin da ke tsakanin N5,500 ko sama a yankuna daban-daban na Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda tsadar simintin yake

Sai dai, ana danganta rashin saukar simintin da wasu lamurran da suka shafi kasuwancin yau da kullum, ciki har da cire tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta yi.

Binciken jaridar BusinessDay ya bayyana cewa, yankuna daban-daban na kasar nan na siyar da simintin a farashinsa na baya.

Manyan masu harkallar siminti a yankin Nyanya a Abuja sun bayyana cewa, har yanzu ragin bai yi wani tasiri ba, domin ana siyar da simintin na BUA da Dangote a farashinsu na baya.

A Fatakwal, an gaza samun simintin BUA, amma akwai na Dangote da ake samu a farashin da bai yi kasa da N5,600 ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi basarake har fadarsa sun dauki ransa a arewacin Najeriya

Har yanzu kamar jiya

A birnin Benin, masu harkalla siminti sun ce, har yanzu basu sauya farashin na BUA ba, inda suka ce ana siyar dashi daga N4,500 zuwa N5,500.

A Kudu maso Gabashin Najeriya, akan rasa simintin BUA ko kuma a same shi da matukar tsada fiye da sanarwar da kamfanin ya fitar.

Ba a samu simintin BUA a jihohin Legas da sauran Kudu maso Yamma ba, duba da wasu manyan wurare hudu kamar haka; Adeniji Adele a tsibirin Lagos, Ketu a Ojo, Ikotun-Egbe a Alimosho, da kuma Suru Alaba a Ajeromi Ifelodun.

Silar tsadar simintin BUA

Wani masani a ma'aikatar binciken kudi da kasuwanci ta CSL Stockbrokers Limited ya danganta tsayuwar farashin a yadda yake a baya da tsadar safaran kayayyaki.

A cewarsa, hakan ba zai rasa nasaba da cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi ba.

Ya zuwa zuwa yanzu dai kusan komai a kasuwannin Najeriya na kara farashi, siminti bai tsira ba daga kayayyakin da ke ci gaba da kara farashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel