Dan Najeriya Ya Nemo Aikin da Ake Biyan Albashi Miliyan 2.6 Duk Wata a Lagas, WAEC Kawai Ake Bukata

Dan Najeriya Ya Nemo Aikin da Ake Biyan Albashi Miliyan 2.6 Duk Wata a Lagas, WAEC Kawai Ake Bukata

  • Wani matashi dan Najeriya ya sanar da cewar ofishin jakadancin Amurka a Lagas, Najeriya, yana neman wanda zai taimaka da aikace-aikace a ofis da albashi ₦2,699,000 duk wata
  • Takardar shaidar kammala sakandare wato SSCE ne mafi karanci da ake bukata, amma za a fi son wanda ya mallaki kwalin gaba da sakandare da kuma kwarewa a turanci
  • Za a kulle neman aiki a ranar 1 ga watan Fabrairun 2024, kuma wadanda ke sha'awar aikin na iya ziyartan shafin yanar gizo na ofishin jakadancin Amurka don karin bayani

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani matashi dan Najeriya ya yiwa jama'a tayin aiki mai tsoka a ofishin jakadancin Amurka da ke Lagas, Najeriya, wanda ke nuni da cewar akwai gurbin aiki na wanda zai taimaka da aikace-aikace a ma'aikatar

Kara karanta wannan

An kama wani mutum bayan ya ziyarci surukansa ba tare da sadaki ba, sun dafa abinci da komai na biki

Wanda ya yi nasarar samun aikin zai kasance yana gudanar da ayyukansa a karkashin sashen ba da shawarwari na ma'aikatar.

Dan Najeriya ya yi tayin aiki da albashi mai tsoka
An yi amfani da hoton don misali ne kawai Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ayyukan da zai rinka yi sun hada da tsara ganawar jama'a da sashen ma'aikatar, samar da takardar biza ga jama'a da kuma adana bayanan duk ayyukan da ya ke yi a cikin kundin ajiyar ma'aikatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashin wannan mukamin shine ₦2,699,000 duk wata, wanda ya yi daidai da kimanin $2,500. Abun da ake bukata shine takardar shaidar kammala karatun sakandare (SSCE), amma za a fi son wadanda suka mallaki kwalayen OND, HND, ko digiri.

Za a rufe neman aikin wannan mukami a ranar 1 ga watan Fabrairun 2024.

Kalli wallafar a kasa:

Guraben aiki da albashi mai tsoka

A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta kawo a baya cewa wani dan Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa akwai guraben aiki da za a biya albashin naira miliyan uku duk wata.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Mutumin mai amfani da sunan @3mbeeeee a Twitter ya bayyana cewa a Abuja ake yin aikin kuma kamfanonij na neman kwararru da za su kama aiki nan take.

Sai dai da yawa ba su gamsu da wannan bayanin na sa ba, inda daga bisani ya wallafa adireshin neman aikin don tabbatarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng