“Ke Yar 419 Ce”: Budurwa Ta Ki Kaiwa Saurayi Ziyara Abuja Bayan Ta Karbi 20k Kudin Mota, Ya Fusata

“Ke Yar 419 Ce”: Budurwa Ta Ki Kaiwa Saurayi Ziyara Abuja Bayan Ta Karbi 20k Kudin Mota, Ya Fusata

  • Wata matashiya yar Najeriya ta ce ba za ta iya yin tattaki har Abuja don ganin saurayi da N20k a matsayin kudin mota ba
  • Mutumin Abujan da ya aike mata da kudi ya fusata sannan ya ce abun da budurwar ta yi masa daidai yake da damfara
  • Sai dai kuma, matashiyar ta ce kudin ya yi kadan sannan ta bayyana cewa mutumin ya yankar mata tikitin jirgin sama

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani mutumi da ya turawa budurwa kudin N20,000 domin ta yi kudin motar zuwa ganinsa a Abuja ya nuna fushinsa saboda ta ki zuwa.

A wata wallafa da ta yi a TikTok, an jiyo muryar mnutumin yana kiran budurwar a matsayin yar 419.

Kara karanta wannan

An kama wani mutum bayan ya ziyarci surukansa ba tare da sadaki ba, sun dafa abinci da komai na biki

Budurwa ta ci kudin saurayi
“Ke Yar 419 Ce”: Budurwa Ta Ki Kaiwa Saurayi Ziyara a Abuja Bayan Ta Karbi 20k Kudin Mota Hoto: TikTok/@ukhaylove4.
Asali: TikTok

Mutumin ya ce lallai sai dai yarinyar ta yi kokarin daina dabi'arta na karbar kudi daga wajen maza sannan ta ki kai masu ziyara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma budurwar mai suna Nancy a TikTok, ta dage cewa kudin ya yi kadan kuma ba za ta iya zuwa Abuja da shi ba.

Bata bayyana inda take ba amma dai ta bayyana a sashin sharhi cewa kamata ya yi ace mutumin ya yankar mata tikitin jirgin sama.

Ta rubuta:

"Ta yaya zan yi amfani da 20k kan kudin motar zuwa ganin namiji? Har zuwa Abuja? Asiri ne wannan? Ba su shirya ba har sai sun yanki tikitin jirgin sama."

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@adunnyyyade ta tambaya:

"Ta yaya N20k zai kai ki zuwa Abuja?"

@Biju-Xoxo ta ce:

"Kin jefa kanki a gagarumin matsala."

Kara karanta wannan

"Ban iya bacci ba": Budurwa ta fashe da kuka bayan ta gano saurayinta na shekaru 3 ya yi aure

@Amaberry ta ce:

"Kin yi kokari yar'uwa. Mu da muke Abuja ba za ba mu ko sisi. Bayan mun ziyarce su, babban abun da za su baka shine 1k."

@MMA ta ce:

"Ina alfahari da ke mami. Na ci 50k yi tunanin barin Lagas zuwa Abuja. Masu garkuwa da mutane su je su kama ni. Me zan fada ma mahaifiyata."

An kama dattijo saboda sadaki

A wani labari na daban, mun ji cewa wani al'amari ya afku a yankin Bukwo, inda wani mutum mai suna Samuel Maikut, ya je gidan surukansa ba tare da kudin sadakin da ake sa ran zai kawo ba, lamarin da ya dimauta dangin amaryar tare da fusata su.

Kamar yadda Ugandan Monitor ta rahoto, Maikut ya fada ma dangin cewa yana so ya auri diyarsu a aure irin na gargajiya sannan ya bukaci da su yi komai na shagalin bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng