Abba Kabir Ya Saduda, Ya Amince da Biyan Kudaden Diyyar Rusau, an Bayyana Adadinsu

Abba Kabir Ya Saduda, Ya Amince da Biyan Kudaden Diyyar Rusau, an Bayyana Adadinsu

  • Gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya kudade har naira biliyan 3 kudin diyyar wadanda aka yi wa rusau a jihar
  • Gwamnan zai biya kudaden ne ga masu shaguna a masallacin Idi da kuma kungiyar 'yan kasuwa a Kano
  • Tun farko, 'yan kasuwar sun bukaci biliyan 250 daga gwamnatin jihar inda kotu ta tsayar da shi kan biliyan 30

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - A karshe, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sallama inda ya amince da biyan kudin diyyar rusau a jihar.

Abba ya amince da biyan naira biliyan uku don diyyar rusau na shagunan masallacin Idi da kungiyar 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mazauna garin Tudun Biri sun karyata kai karar gwamnatin Tinubu kotu

Abba Kabir ya amince da biyan diyyar rusau a Kano
Abba Kabir zai biya kudin diyyar rusau biliyan uku. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Wane yarjejeniya aka kulla da Abba?

Wannan na zuwa ne bayan kulla yarjejeniya a gaban alkalin babbar Kotun Tarayya a jihar a jiya Laraba 13 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun ranar Talata ce dai aka kulla yarjejeniyar a takarda da sa hannun lauyoyin ko wane bangare a gaban alkali, Inyang Ekwo.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar 'yan kasuwar da masu shaguna sun maka Gwamna Abba Kabir a kotun, cewar Daily Trust.

Wane hukunci kotun ta yanke kan rusau?

Yayin yanke hukuncin, Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta umarci gwamnan ya biya biliyan 30 madadin biliyan 250 da 'yan kasuwar su ka bukata.

Bayan gwamnatin jihar ta ki biyan kudaden, sai 'yan kasuwar su ka sake shigar da kara a gaban Alkalin kotun, Inyang Ekwo don bi musu kadunsu, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Duk da jerin alkawura, 'yan Tudun Biri sun kai karar Gwamnati a Kotu ana neman N33bn

Daga cikin wadanda kungiyar ta shigar kara akwai gwamnatin jihar da kwamishinan Shari'a, da Babban Sifetan 'yan sanda da hukumar tsara muhalli a jihar.

Kotu ta rufe asusun bankunan gwamnatin Kano

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta rufe asusun bankunan gwamnatin jihar Kano 24 kan kudaden diyyar rusau a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta umarci Gwamna Abba Kabir na jihar ya biya naira biliyan 30 ga wadanda abin ya shafa.

Masu shaguna a masallacin Idi da kungiyar 'yan kasuwa sun maka gwamnan a kotu don ya biyan su biliyan 250 na diyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.