Cikakkun Jerin Manyan Jami’an Gwamnati 9 da Tinubu Ya Tsige Cikin Sa’o’i 24

Cikakkun Jerin Manyan Jami’an Gwamnati 9 da Tinubu Ya Tsige Cikin Sa’o’i 24

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsige akalla manyan jami'an gwamnati tara tsakanin Laraba da Alhamis, 13 da 14 ga watan Disamba
  • Gwamnatin baya ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta nada wasu daga cikin jami'an da abun ya shafa
  • Manyan jami'an da abun ya shafa sun kasance shugabannin hukumomi da daraktoci a ma'aikatar sufurin jiragen sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Har yanzu Shugaban kasa Bola Tinubu bai gama tsige manyan jami'an gwamnati tare da nada sabbi ba watanni shida bayan ya karbi ragamar shugabanci.

Gwamnatin da ta shude ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta nada wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin da abun ya shafa.

Shugaban kasa Tinubu ya tsige manyan jami'an gwamnati
Cikakkun Sunayen Manyan Jami’an Gwamnati 9 da Tinubu Ya Tsige Cin Sa’o’i 24 Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Dalilin da ya sa Tinubu ya tsige wasu manyan jami’an gwamnati 9 cikin sa’o’i 24

Kara karanta wannan

Yanzu: Tinubu ya yi kokarin sulhu tsakanin Wike da Fubara, APC ta yi karin haske

A wani lamari mai kama da guzuri yayin da karshen shekara ke gabatowa, Shugaba Tinubu ya tsige akalla mutane tara da suka ci moriyar mukamai a gwamnatin baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan jami’an gwamnatin da abin ya shafa sun hada da shugabannin hukumomin gwamnati, da daraktoci a ma’aikatar sufurin jiragen sama.

A cewar fadar shugaban kasa, ci gaban ya yi daidai da tsarin mulkin Najeriya da kuma sabon ajandarsa na sabonta fata. Manyan daraktocin tara su ne na baya-bayan nan da Tinubu yake kora tun bayan hawansa mulki kimanin watanni bakwai da suka gabata.

Ga jerin sunayen manyan jami'an gwamnati da abun ya shafa

  1. Mista Kabir Yusuf Mohammed, Shugaban hukumar FAAN
  2. Mista Tayib Adetunji Odunowo, Shugaban hukumar NAMA
  3. Injiniya Akinola Olateru, shugaban hukumar NSIB
  4. Farfesa Mansur Bako Matazu, Shugaban hukumar NIMET
  5. Kyaftin Alkali Mahmud Modibbo, Shugaban kwalejin fasahar jiragen sama ta Najeriya (NCAT)
  6. Daraktan hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NIMET)
  7. Daraktan hukumar kula da sararin samaniyar Nijeriya (NAMA)
  8. Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA)
  9. Daraktan hukumar binciken sufurin jirage (NSIB)

Kara karanta wannan

"Ainahin dalilin da yasa muka tsige gwamna da yan majalisar PDP 16": Alkalin kotun daukaka kara

Tinubu ya sallami daraktoci 5

A wani labarin, mun ji a baya cewa kasa da awanni 24 da korar shuagabannin hukumomin jiragen sama, Tinubu ya kori dukkan daraktocinsu.

A jiya ne Shugaba Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin FAAN da NAMA tare da maye gurbinsu, cewar The Nation.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng