Kungiyar ECOWAS Ta Hakura, Ta Bada Sharuda 2 Kafin Cire Takunkumi a Kan Kasar Nijar
- Africans Without Borders ta kai ziyara zuwa majalisar ECOWAS domin ganin an cire takunkumi a kan kasar Nijar
- Majalisar kungiyar ECOWAS ta ce kafin a sassauta, wajibi ne sojojin da ke rike da iko su fito da Mohammed Bazoum
- ECOWAS ta bukaci sakin Bazoum da iyalinsa, sannan a fara shirye-shiryen mikawa farar hula mulki a jamhuriyyar
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Shugaban majalisar kungiyar ECOWAS, Sidie Tunis ya ce za a janye takunkumin da aka kakabawa Nijar amma da sharadi.
Sidie Tunis ya yi wannan bayani ne a lokacin da tawagar ‘Africans Without Borders’ ta kai masa ziyara a jiya, Tribune ce ta fitar da rahoton.
‘Yan Africans Without Borders sun ziyarci shugaban majalisar kungiyar kasashen Afrikan ne a kan maganar halin da Nijar ta ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sharadin kyale Mohamed Bazoum
A yayin ganawar da aka yi a birnin tarayya Abuja, Sidie Tunis ya fadawa Africans Without Borders ta dage a saki Mohamed Bazoum.
Idan aka kyale Mohamed Bazoum kuma iyalinsa su ka samu ‘yanci sannan aka shirya mika mulki, za a sassautawa jamhuriyyar Nijar.
Majalisar ta ECOWAS ta ce dole sojojin da su ka hambarar da Bazoum su tsaida lokacin mika mulki ga fararen hula a kasar Afrikar.
Daily Trust ta rahoto Tunis yana kukan cewa duk kokarin da ake ta yi, ba ayi nasara a kan sojojin da su ka kifar da gwamnatin Nijar ba.
Yadda za a taimaki kasar Nijar
Majalisar ta ce sojojin da su kayi juyin mulki ne za su iya kawo karshen halin da aka shiga wanda Sanatocin Najeriya sun soki lamarin.
Tunis ya ce yanayin Nijar yana damunsu kuma ana son magance matsalolinta da sauran kasashen, amma sai kowa ya bada gudumuwa.
Ziwana Abdounahamane wanda ya yi magana a madadin kungiyar, ya ce takunkumin ya shafi sauran kasashe da ke kusa da Nijar.
Sanusi II ya yi kira ga ECOWAS
A kwanakin bayan nan aka rahoto Muhammadu Sanusi II ya ce ECOWAS ta biyewa kasashen Yamma, ana ta azabtar da mutanen Nijar.
Sarkin Kano na 14 ya ce ana kallon Israila tana kashe Falasdinawa dare da rana ba ayi komai ba, amma an sa takunkumi a Jamhuriyyar
Asali: Legit.ng