Yan Sanda Sun Halaka Yan Bindiga 13 Da Ceto Mutum 268 Da Aka Sace
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta bayyana nasarar da ta wajen yaƙi da ƴan bindiga a cikin watanni huɗu
- A tsakanin watan Yuni zuwa watan Satumba rundunar ta halaka ƴan bindiga 13 tare da ceto wasu mutum 268 da aka sace
- Kakakin rundunar ƴan sandan wanda ya tabbatar da hakan ya kuma ce an ƙwato bindigogi, ƙwayoyi da dabbobi a hannun miyagun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta halaka mutum 13 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar.
Rundunar ta kuma ce ta kuɓutar da mutum 268 da aka yi garkuwa da su a lokuta daban-daban daga watan Yuni zuwa watan Satumba na wannan shekara, cewar rahoton Leadership.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya fitar a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, ya ce a daidai wannan lokacin, an kama kimanin mutum 104 da ake zargi da aikata fashi da makami.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ya ƙara da cewa an kuma kama mutum 97 da ake zargi da laifin kisan kai, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa an kama mutum 148 da ake zargi da aikata laifin fyade, sannan kuma an kama mutane bakwai da laifin mallakar haramtattun ƙwayoyi.
Rundunar ta ƙwato kayayyaki a hannun ƴan bindiga
Har ila yau, a cikin wannan lokacin an ƙwato kayayyaki da suka haɗa da ƙaramar bindiga guda ɗaya, da harsasai 523.
ASP Aliyu ya cigaba da bayanin cewa, sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu, bindigu na gida guda shida.
Sauran sun haɗa da dabbobi sama da 600 da aka sace, motoci da babura 12 da ake zargin na sata ne da wayoyin hannu guda 17 da ake zargin na sata ne.
A cewarsa, wasu haramtattun ƙwayoyi da aka kwace a lokacin da ake binciken sun haɗa da buhu 568 na D5, ƙulli 180 na tabar wiwi, fakiti 23 na ƙwayar Exzole, fakiti 411 na ƙwayar Rebozel, da fakiti biyar na ƙwayar Diezole.
Ƴan sanda sun yi ƙoƙari
Faisal Sulaiman wani mazaunin jihar Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa abin da ƴan sandan suka yi abun a yaba ne. Ya jinjina musu kan wannan nasarar da suka samu tare da kira ga gwamnati da ta ƙara ƙarfafa musu gwiwa.
"Abu ne mai kyau gaskiya sun yi ƙoƙari wannan abin da suka yi. Ya kamata gwamnati ta ƙara ƙarfafa musu gwiwa kan wannan jajircewar da suke yi." A cewarsa.
Ya kuma yaba da yadda ake cigaba da samun tsaro a jihar Katsina, inda ya ce abubuwa suna yin kyau sosai yanzu ta fannin tsaro a jihar.
Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Dillalan Jaridu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban dillalan jaridu na babban birnin tarayya Abuja.
Ƴan bindigan sun sace Mista Emmanuel ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, inda suka buƙaci a ba su N15m matsayin kuɗin fansa.
Asali: Legit.ng