“Ka Siyar Ka Rasa Kujerar Ka”: Gwamnatin Kebbi Ta Gwangwaje Kwamishinoni da Motocin Alfarma

“Ka Siyar Ka Rasa Kujerar Ka”: Gwamnatin Kebbi Ta Gwangwaje Kwamishinoni da Motocin Alfarma

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta sha alwashin korar duk wani kwamishina da ya siyar da motar da gwamnatin ta ba shi
  • Gwamnan jihar Nasiru Idris ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin mika motocin ga kwamishinoni 26 na jihar
  • Gwamnan ya ce an siya wa kwamishinonin motar ne don gudanar da ayyukan ofishinsu ba wai don amfanin kansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kebbi - Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi a ranar Laraba ya ce ba zai yi kasa a guiwa ba wajen korar duk kwamishinan da ya sayar da motar da gwamnatin jihar ta ba su.

Ya sha alwashin korar korar duk wanda a cikinsu ya daina ziyartar mazabarsa don jin hali da al'umma suke ciki kan tsare-tsaren gwamnatin sa.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mazauna garin Tudun Biri sun karyata kai karar gwamnatin Tinubu kotu

Gwamnatin Kebbi ta gwangwaje kwamishinoni da motocin alfarma.
Gwamnan Kebbi, Nasiru Idris ya ce duk wani kwamishina da ya siyar da motar da gwamnati ta ba shi zai rasa aikin sa. Hoto: Kaura_Movement
Asali: Twitter

Dalilin da ya sa aka ba kowanne kwamishina mota - Gwamnan Kebbi

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a Birnin Kebbi yayin da ya ke mika kyautar motocin aiki guda 26 ga kwamishinonin jihar da gwamnati ta siya, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sa:

"Wadannan motocin da muka ba ku do su taimaka maku wajen ziyartar jama'arku akai-akai, tare da kawo mana rahoton bukatunsu ko abin da suke so mu yi.
"Ba zan ragawa duk kwamishinan da ya siyar da motar da muka ba shi ba, zan tsige shi daga mukami nan take."

Gwamnan ya kuma raba babura 700 ga mambobin kungiyar 'yan sa kai domin basu damar gudanar da ayyukansu na tsaro yadda ya kamata.

Gwamnatin jihar ta wallafa hotunan ababen hawan a shafinta na Twitter wanda ta raba wallafar da shafin Kauran gwandu ya yi, duba a kasa:

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gobara ta kama ofishin gwamnan jihar Borno

Gwamnati ta rushe ginin majalisar jihar Rivers, ta fadi dalili

A wani labarin, gwamnatin jihar Rivers ta ce ta rushe ginin majalisar dokokin jihar don gina sabuwa, biyo bayan wata gobara da ta lalata wani bangaren na majalisar.

A cewar gwamnatin, 'yan majalisun jihar ba za su iya zama a cikin zauren majalisar ba saboda hatsari da ke tattare da ginin, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin 2024 ga majalisar Rivers

A jiya Laraba ne gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya gabatar wa majalisa kasafin kudin 2024 na jihar da ya kai Naira biliyan 800.

Majalisar ta yi zamanta na jiya a wani matsugunnin wucin gadin da aka ba ta a cikin fadar gwamnatin jihar, kafin a gina sabon zauren majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.