‘Yan Sanda Sun Damke Wasu Jami’ai 3 Za Su Yi Gwanjon Kayan Gwamnati a Jihar Kano
- Rundunar yan sanda na jihar Kano ta ka wani Darekta na harkar gudanarwa da ayyuka a ma’ikatar ruwa
- Abubakar Gambo da wani tsohon abokin aikinsa suna fuskantar bincike a kan daukar kayan gwamnati
- An rubuta takarda domin yin gwanjon dukiyar jama’a, kwamishinan ruwa ya ce shi dai ba da sunansa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa an cafke wasu ma’aikata da zargin shirin karkatar da kayan al’umma.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Hussaini Gumel ya shaidawa Daily Trust cewa wadannan jami’ai suna hannu, kuma ana bincike.
Wadanda aka kama sun hada Darektan gudunarwa da ayyukan yau da kullum na ma’aikatar harkar ruwa, Alhaji Abubakar Gambo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan akwai Baba Yahaya wanda mataimakin sakataren gudanarwa ne a ma’aikatar harkokin ruwa na gwamnatin jihar Kano.
Na ukunsu shi ne wani tsohon shugaban hukumar tsarin noman rani na KAREFA a karamar hukumar Tudun Wada, Nuhu Mansir.
An samu izinin saida kayan gwamnati a Kano
‘Yan sanda sun cafke su ne bisa zargin rubuta wasikar bogi da ta bada izinin yin gwanjon wasu kaya irinsu tanki da injin rabba ruwa.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce ana tuhumar jami’an gwamnati da yin awon gaba da dukiyar al’umma, wanda hakan ya sabawa doka.
Kano: Kwamishina ya ce babu ruwansa
Tashar Nasara FM ta ce da aka tuntubi Kwamishinan harkar ruwa, Ali Makoda, ya nuna ba ta hannun shi aka fitar da takardar nan ba.
A sakamakon bayanin da aka samu daga Makoda, aka samu kwarin gwiwa cewa ma’aikatan sun karkatar da dukiyar jihar Kano ne.
Da zarar an gama bincike, kwamisinan ‘yan sandan da ya dage wajen ganin bayan miyagu a Kano ya ce za su gurfanar da su a kotu.
Facakar kudi a gwamnatin tarayya
A gwamnatin tarayya, an ji labari Ministar kasuwanci ta shirya kashe kusan N9bn a 2024, amma ‘Yan Majalisa sun yi mata kaca-kaca.
A shekara mai zuwa, Doris Uzoka-Anite ta yi niyyar zuwa birnin Geneva, za a kashe N1bn a tafiyar, hakan ya sa aka taka mata burki.
Asali: Legit.ng