Yanzu Yanzu: Ganduje ya nada Makoda a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati

Yanzu Yanzu: Ganduje ya nada Makoda a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nada tsohon kwamishinansa na muhalli, Ali Haruna Makoda a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati wato 'Chief of Staff (COS).

An bayyana nadin ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar a ranar Alhamis a Kano.

Gwamnan ya mika sakon taya murnarsa ga wanda aka yi wa nadin sannan ya bukaci shi da ya cigaba da jajircewa wurin yi wa al'ummar jihar hidima.

DUBA WANNAN: Za a gamu da munanan bala'o'i na ambaliyar ruwa a jihohi 30 - NIHSA

Gwamnan ya kuma yi amanna da irin gudunmuwar da Mokoda ya bayar wurin cigaban jihar kuma ya jinjina masa bisa nasarorin da ya samu a matsayinsa na kwamishina a zagon mulkin farko na gwamnatinsa.

"Ali Haruna Makoda mutum ne mai matukar daraja a jihar mu. Hakan ya sa akwai bukatar a cigaba da tafiya da shi a zangon mulki na karo na biyu," a cewar gwamnan.

Makoda ya yi karatun digirinsa na farko a fanin Libarary da Kimiytar siyasa sannan ya yi karatun digiri na biyu a fanin Tafiyar da kasuwanci a Jami'ar Bayero ta Kano kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel