Babbar Magana: EFCC Ta Fara Neman Tsohon Minista Agunloye Ruwa a Jallo, Ta Fadi Dalili

Babbar Magana: EFCC Ta Fara Neman Tsohon Minista Agunloye Ruwa a Jallo, Ta Fadi Dalili

  • Hukumar EFCC ta ce ta baza komar kama Olu Agunloye, tsohon ministan makamashi da karafa karkashin gwamnatin Obasanjo
  • A cewar hukumar da ke yaki da masu satar dukiyar al'umma, duk wanda ya ci karo da Agunloye, ya sanar da hukuma mafi kusa
  • A baya ne EFCC ta titsiye tsohon ministan kan sa hannunsa a badakalar $6bn na kudin kwangilar gina tashar wutar lantarki ta Mabila

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Hukumar da yaki da masu yi wa dukiyar al'umma zagon kasa (EFCC) ta ayyana Olu Agunloye, tsohon ministan makamashi da karafa matsayin wanda take nema ruwa a jallo kan zargin rashawa.

Agunloye ya rike mukamin minista karkashin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake ofisoshi akalla 17 a sakateriyar ƙaramar hukuma 1 a jihar Kano

EFCC/Olu Agunloye
EFCC na neman tsohon minista Agunloye ruwa a jallo. Hoto: Olu Agunloye
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a yammacin ranar Talata, EFCC ta nemi 'yan Najeriya su sanar da hukuma mafi kusa idan sun ci karo da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta tuhumi Olu Agunloye, ministan Obasanjo kan makamashi da karafa

EFCC ta taba gayyatar Agunloye don tambayoyi kan sa hannunsa a wata badakalar dalar Amurka biliyan shida na aikin tashar wutar lantarkin Mambila.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya zargi Agunloye da karkatar da kudin aikin inda ya gaza kare kansa bayan da majalisar zartaswar gwamnatin tarayya ta nada shi minista.

Obasanjo ya kalubalanci tsohon ministan ya fito ya sanar da 'yan Najeriya yadda aka yi da kudin kwangilar da ya ba kamfanin 'Sunrise Power and Transmission'.

Olu Agunloye ya yi wa Obasanjo martani kan aikin wutar Manbila

Kara karanta wannan

Cibiyar samar da wutan lantarkin Najeriya ta sake durkushewa a karo na uku

A nashi bangaren, Agunloye ya yi ikirarin cewa a shekarar 2003 ne aka ba ofishinsa aikin gidanawa, some aiki da mika wa na tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla.

A cewarsa, gwamnati ba ta biya kamfanin Sunrise ko sisi ba na gina tashar wutar lantarkin, saboda kamfanin shi ya dauki nauyin aikin da kudin sa, rahoton Premium Times.

Duba sanarwar a nan:

Karo a uku, ibiyar wutar lantarkin Najeriya ta durkushe

A wannan makon ne muka kawo maku wani rahoto na yadda cibiyar wutar lantarkin Najeriya ta durkushe, wanda ya jefa kasar cikin duhu na dan wani lokaci.

Ba wannan ne karo na farko ba, ko a cikin watan Satumba sai da cibiyar ta durkushe har sau biyu, lamarin da ya jefa 'yan Najeriya cikin jefa alamar tambaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.