Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji 4 a Wani Sabon Hari, Bayanai Sun Fito

Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji 4 a Wani Sabon Hari, Bayanai Sun Fito

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan ayarin motocin wani kamfanin mai a jihar Rivers
  • Ƴan bindigan waɗanda suka yi wa ayarin motocin kwanton ɓauna sun halaka jami'an sojoji huɗu da sace wasu ƴan ƙasar waje mutum biyu
  • Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da aukuwar mummunan harin inda ta ce jami'an ta na ƙoƙarin cafke ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Wasu ƴan bindiga sun yi wa ayarin motocin wani kamfani kwanton ɓauna a tsagin Ahoada/Abua na titin hanyar Gabas-Yamma a jihar Rivers.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe sojoji hudu da direbobi biyu tare da sace wasu ƴan kasashen waje biyu da aka bayyana su a matsayin ƴan ƙasar Koriya.

Kara karanta wannan

Mako ɗaya bayan jefa bam a Kaduna, 'yan bindiga sun ƙara yin mummunar ɓarna kan bayin Allah

Yan bindiga sun halaka sojoji a Rivers
Rundunar sojin Najeriya ta rasa sojoji hudu a jihar Rivers Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Yadda harin ya auku

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, an ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9.30 na safiyar ranar Talata, 12 ga watan Disamba, yayin da kamfanin ke jigilar ma'aikatansa zuwa wani sansani da ke Yenagoa a jihar Bayelsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin dai ya haifar da tashin hankali da shiga halin ɗar-ɗar a yankin, a cewar jaridar The Nation.

Wata majiyar tsaro da ta yi magana cikin ƙwarin gwiwa ta ce waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi wa ayarin motocin kwanton ɓauna, inda nan take suka buɗe wuta kan mutanen.

"A yayin harin, maharan sun buɗe wuta kan ayarin motocin inda suka kashe sojoji huɗu da direbobi fararen hula biyu sannan suka yi awon gaba da wasu ƴan Koriya mutum biyu." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki a fada, sun yi awon gaba da babban basarake

"Har yanzu babu cikakkun bayanai amma ana cigaba da ƙoƙarin samun ƙarin bayanai. Za a gabatar da ƙarin cikakkun bayanai nan ba da jimawa ba."

Rundunar Sojojin Najeriya ta mayar da martani

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana lamarin a matsayin wanda bai dace ba.

Rundunar ta sha alwashin cewa za a kama wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Mataimakin daraktan riƙo, jami’in hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, Manjo Danjuma Danjuma a wata sanarwa da ya fitar ya ce wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai harin.

Wani ɓangare na sanarwar cewa:

"Dakarun Bataliya 5 da ke aikin rakiya na yau da kullum na wani kamfani mai kula da mai a Enweh West manifold, ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas ta jihar Ribas, wasu da ake zargin ƴan bindiga sun kai musu hari, a mahadar Emesu, kan hanyar Amungboro-Emuphan."

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun kashe mutum 3

"Sai dai abin takaicin shi ne, an kashe sojoji hudu a harin, tare da wasu ma’aikatan mai guda biyu da ba a san inda suke ba."
"Ana zargin ƴan bindigan sun tsere ne ta gaɓar ruwan Emesu, ta hanyar amfani da kogin Orashi. A halin yanzu dai sojoji na cigaba da yi wa yankin ƙawanya domin zakulo wadanda suka aikata wannan ɗanyen aikin."

Matawalle Ya Yabi Sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yaba wa dakarun sojoji bisa halaka ƴan bindiga 30 a jihar Neja.

Dakarun sojojin a yayin wani farmaki da suka kai sun halaka ƴan bindigan ciki har da wasu gawurtattun ƴan bindiga mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng