Matawalle Ya Yi Wani Muhimmin Abu 1 Ga Sojoji Bayan Sun Halaka Yan Bindiga 30 a Neja

Matawalle Ya Yi Wani Muhimmin Abu 1 Ga Sojoji Bayan Sun Halaka Yan Bindiga 30 a Neja

  • Ƙaramin ministan tsaro ya yabawa rundunar sojin Najeriya kan nasarar da ta samu wajen kakkabe ƴan bindiga sama da 30 da suka haɗa da Ali Kawajo da Shehu Rakef
  • An bayyana Ali Kawajo a matsayin wanda ya shirya harin bam a jirgin ƙasan Kaduna tare da yin garkuwa da fasinjoji sama da 100 a shekarar 2022
  • Matawalle ya yabawa babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar TA Lagbaja da daukacin sojojin Najeriya, inda ya buƙace su da su ci gaba da ƙoƙarinsu na yaƙi da ta'addanci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Bello Muhammad Matawalle, ƙaramin ministan tsaro, ya yabawa rundunar sojin Najeriya bisa nasarar da ta samu a kusa da Tungar Mangwaro a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Mako ɗaya bayan jefa bam a Kaduna, 'yan bindiga sun ƙara yin mummunar ɓarna kan bayin Allah

Ministan, a wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng, ya yabawa rundunar musamman kan yadda ta kashe ƴan bindiga sama da 30 a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba.

Matawalle ya yaba wa sojojin Najeriya
Matawalle ya yaba kan kisan da sojoji suka yi wa yan bindiga a Neja Hoto: @BelloMatawalle1
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa an kashe wasu fitattun ƴan bindiga guda biyu, Ali Kawajo da Shehu Rakef a yayin farmakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene Ali Kawajo da Shehu Rakef?

Rahotanni sun bayyana cewa Ali Kawajo ne ya shirya harin bam na jirgin ƙasa tare da yin garkuwa da fasinjoji sama da 100 a shekarar 2022 da kuma sace ɗaliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara kwanan nan.

Duka Ali Kawajo da Shehu Rakef, a cewar sanarwar, suna da hannu dumu-dumu cikin ayyukan ƴan ta’adda a jihohin Kaduna, Neja da Zamfara, musamman kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Matawale musamman ya taya babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar TA Lagbaja da rundunar sojojin Najeriya baki daya murnar wannan gagarumar nasara da suka samu tare da ƙara musu kwarin gwiwa da kada su gajiya a ƙoƙarinsu na yaƙi da rashin tsaro a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame fadar babban sarki, sun kwato makamai

Ƴan Bindiga sun sace Basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a fadar babban basaraken Akpabuyo da ke jihar Cross Rivers.

Ƴan bindigan a ya yin farmakin sun halaka hadimin basaraken mutum ɗaya tare da yin awon da basaraken.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng