Na kan yi dariya idan na ji ana cewa ba a son mace mai kiba - Dirarriyar budurwa

Na kan yi dariya idan na ji ana cewa ba a son mace mai kiba - Dirarriyar budurwa

- Wata dirarriyar budurwa ta yi wata wallafa wacce ta kawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Facebook

- Budurwar ta wallafa hoton ta, inda tace mutane da dama sun ce mata masu kiba dumama gado kadai suka iya

- A cewarta, kowacce mace tana da kyau duk yadda surarta ko dirinta yake, mutane su canja tunani

Wata dirarriyar budurwa, 'yar Najeriya tace tana cin dariya idan taji mutane na cewa mata masu kiba sunfi dadin dumama gado amma ba aure ba.

Budurwar ta wallafa hotonta a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda tace ya kamata a ce mutane sun canja tunaninsu, su san cewa kowacce mace tana da kyau na musamman.

Kamar yadda ta wallafa, "Yana matukar bani dariya idan naji mutane suna cewa mata masu kiba suna da dadin abota da kuma dumama gado, amma basu da dadin aure. Ina so kowa ya canja tunaninsa yau! Kowacce mace tana da kyau da salo ko yaya surarta da fatarta take."

KU KARANTA: 2023: INEC ta fitar da N1bn, ta sanar da ranar cigaba da yi wa masu zabe rijista

Na kan yi dariya idan na ji ana cewa ba a son mace mai kiba - Dirarriyar budurwa
Na kan yi dariya idan na ji ana cewa ba a son mace mai kiba - Dirarriyar budurwa. Hoto daga Shomie Thickana
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ciyar da 'yan makaranta: Ganduje yana kashe N4bn kowacce shekara - Kwamishina

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe sansanin 'yan gudun hijira a ranar Laraba a jihar, kuma ta umarci mutane 27,000 su koma kauyukansu.

Kwamishinan matasa da habaka wasanni na jihar, Alhaji Sani Danlami, ya bayyana hakan ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar, inda yace za a rufe sansanin gudun hijirar da ke Dandume, Faskari, Kankara, Batsari, Jibia, ATC Katsina da gidan marasa gata da ke Katsina.

Ya ce an yanke shawarar rufe sansanin ne saboda zaman lafiya da samun tsaro da ya fara tabbata a jihar, The Nation ta wallafa.

Yace; "Gwamnatin jihar ta taimaki 'yan kauyakun, inda tace ya kamata su koma gidajensu su don cigaba da rayuwarsu.

"Yau ba a samu kowa ba a sansanin gudun hijira. Duk da har yanzu muna da labarin wasu da ke yawo a cikin gari da sunan 'yan gudun hijira ne."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng