Daliban Firamare 18 Sun Kwana A Asibiti Kan Cin Abinci da Gwamnati Ke Bayar Wa, an Fadi Dalili
- An samu matsala yayin da daliban firamare 18 su ka kamu da cututtuka bayan cin abincin gwamnati da ta ke bayar wa kyauta
- Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 11 ga watan Disamba a makarantar St. James da ke Osogbo da ke jihar Osun
- Tuni Gwamna Ademola Adeleke na jihar ya ba da umarnin fara bincike kan lamarin tare da daukar nauyin jinyar daliban har su samu sauki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Akalla daliban firamare 18 ne ke kwance a asibiti kan zargin cin gurbataccen abinci a jihar Osun.
Ana zargin daliban firamaren St. James da ke Owo-Ope da ke birnin Osogbo sun ci abincin da gwamnati ke bayar wa ne wa makarantu, Legit ta tattaro.
Mene dalilin samun matsalar daliban?
The Nation ta tattaro cewa yaran sun samu matsala ne bayan cin shinkafa da kwai da masu abincin su ka girka musu a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 11 ga watan Disamba yayin da ake raba abincin kyauta ga daliban.
Daya daga cikin iyayen yaran, Iya Taye mai yara uku a makarantar ta ce dukkansu sun dawo da amai da kuma gudawa.
Iya ta ce yaran sun dawo cikin wani yanayi inda ta ce akwai alamun ana makarkashiya a harkar dafa abincin yaran da gwamnati ke yi.
Wane mataki gwamnati ta dauka?
Ta ce:
"Na kira likita don ya duba lafiyarsu, wasu iyayen sun kai yaransu asibiti, amma ni ina da likitan da ke kula da mu."
Har ila yau, kwamishinan yada labarai a jihar, Kola Alimi ya ce Gwamna Ademola Adeleke ya ba da umarnin binciken gaggawa don gano tushen matsalar.
Alimi ya ce gwamnatin jihar ta dauki nauyin dukkan abin da ake bukata na jinyar yaran da ke samun kulawa a asibitoci.
Gwamnan Osun ya sanya dokar kulle
A wani labarin, Gwamna Ademola Adeleke ya sanya dokar kulle a kananan hukumomi guda 3 a jihar.
Gwamnan ya dauki matakin ne kan rikicin filaye da ya barke a wasu kauyuka a yankin.
Asali: Legit.ng