Gwamnan Jihar Osun Ya Sanya Dokar Kulle a Kananan Hukumomi 2 Na Jihar
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya sanya dokar kulle a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu
- Sanya dokar kullen ya biyo bayan rikicin da ya ɓarke a tsakanin wasu ƙauyuka biyu na ƙananan hukumomin
- Kolapo Alimi, kwamishinan watsa labarai na jihar ya bayyana cewa dokar kullen za ta riƙa aiki ne a tsakanin ƙarfe 8:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, a ranar Lahadi, 17 ga watan Satumba, ya sanya dokar kulle a ƙananan hukumomin Orolu da Irepodum na jihar.
Gwamnan ya sanya dokar kullen ne sakamakon rikicin da ya ɓarke kan filaye a tsakanin ƙauyukan Ilobu da Ifon, na ƙananan hukumomin, cewar rahoton PM News.

Asali: Facebook
Kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Kolapo Alimi, shi ne ya bayyana sanya dokar kullen a cikin wata sanarwa.
Meyasa gwamna Adeleke ya sanya dokar?
Ya bayyana cewa an sanya dokar kullen ne biyo bayan rikicin da ya auku a tsakanin mutanen ƙauyukan Ilobu da Ifon domin tabbatar da doka da oda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin sanarwar, kwamishinan ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ƙarfe 8:00 na kowane dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe, rahoton TheCable ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Hankalin gwamnatin jihar Osun ya kai kan rikicin filaye da ya ɓarke a tsakanin al'ummar ƙauyukan Ilobu da Ifon."
"A dalilin hakan ne gwamna Ademola Adeleke ya bayar da umarnin sanya dokar hana fita nan take a ƙananan hukumomin Orolu da Irepodun."
"Dokar kullen za ta fara aiki ne a tsakanin ƙarfe 8:00 na kowane dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe. Domin haka an hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa yayin dokar kullen har sai abin da hali ya yi."

Kara karanta wannan
Yan Soshiyal Midiya Sun Taso Obasanjo a Gaba Bayan Ya Yi Wa Sarakuna Wani Abu 1 a Bainar Jama'a
Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa duk wanda aka samu da laifin karya dokar, za a kama shi tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Gwamna Ya Sanya Dokar Kulle
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Akwa Ibom, Bassey Otu, ya sanya dokar kulle a wasu ƙauyuka gudu huɗu na jihar.
Gwamnan ya sanya dokar ne biyo bayan rikicin filaye da iyakoki ya ɓarke a tsakanin ƙauyukan masu makwabtaka da juna.
Asali: Legit.ng