Sojin Sama Sun Yi Ajalin Kasurgumin Dan Ta'adda, Kachalla, Sun Hallaka Kwamandojin Dogo Gide 3
- Wasu kasurguman 'yan ta'adda sun gamu da ajalinsu bayan wani hari da sojin sama su ka kai a jihar Niger a jiya
- Daga cikin wadanda su ka mutun akwai kasurgumin dan ta'adda, Kachalla Ali wanda ya addabi jama'a da kuma kwamandojin Dogo Gide
- Wannan na zuwa ne bayan kai hari maboyar Kachalla da Dogo Gide a ranar 6 ga watan Disamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Rundunar sojin saman Nigeriya ta yi nasarar hallaka kasurgumin dan ta'adda, Ali Alhaji Alheri a wani hari a jihar Niger.
Marigayin wanda aka fi sani da 'Kachalla Ali Kawaje' shi ya jagoranci sace daliban Jami'ar Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.
Su waye rundunar ta hallaka yayin harin?
Aminiya ta tabbatar da cewa an kashe Kachalla ne a jiya Litinin 11 ga watan Disamba a jihar Neja yayin wani mummunan harin sojin a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar har ila yau, ta kai farmaki maboyar Kachalla da Dogo Gide a ranar 6 ga watan Disamba ji nada su ka hallaka manyan 'yan ta'adda.
Daga cikin wadanda aka hallakan akwai Machika (kanin Dogo Gide) da Dan Muhammadu, wani hatsabibin mai garkuwa da mutane a sansanin Dogo Gide.
Wane nasara rundunar ta samu kan 'yan ta'addan?
Rundunar ta yi ajalin kaurguman 'yan bindigan uku ne yayin da su ke shirin kai wani hari a jihar Niger.
Dogo Gide da Kachalla sun addabi mutane da dama a jihohin Zamfara da kuma Niger inda su ka yi ajalin jama'a da dama, cewar Leadership News.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan sojin kasa sun kai harin bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.
Rundunar soji ta yi ajalin dan ta'adda a Kebbi
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi ajalin wani kasurgumin dan ta'adda a jihar Kebbi.
Marigayin wanda aka fi sani da Mainasara ya rasa ransa ne yayin wani mummunan hari da sojin su ka yi.
Asali: Legit.ng