Abin da Ya Jawo Ake Wahalar Kudi a Yau – A Karshe Bankin CBN Ya Yi Karin Bayani

Abin da Ya Jawo Ake Wahalar Kudi a Yau – A Karshe Bankin CBN Ya Yi Karin Bayani

  • Babban bankin Najeriya ya fitar da jawabi a kan karancin kudin da ake fama da shi a manyan birane
  • CBN ya yi ikirarin ba kowa ya jawo wahalar kudi a kasar nan ba illa bankunan ‘yan kasuwa da jama’a
  • Sanarwa ta nuna mutane sun dimauce sun yi ta cire kudi daga ATM har kudin da ke yawo su ka ragu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Babban bankin Najeriya wanda da aka fi sani da CBN, ya yi karin haske a kan abin da ya jawo ake wahalar kudi a kasar nan.

Daily Trust ta ce jawabin da aka fitar a karshen makon jiya, ya tabbatar da akwai karancin kudi da ke zagayawa a tsakanin jama’a.

Kara karanta wannan

Ku yi hattara, akwai jabun kudi da ke yawo": Gargadin CBN ga 'yan Najeriya

Gwamnan bankin CBN
Bankin CBN ya yarda babu kudi a kasa Hoto: @Cenbank
Asali: Twitter

Sanarwar da ta fito daga sashen sadarwa na bankin CBN ta ce bankunan kasuwa ne su ka rika cire kudi daga rassan babban bankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a su na ta kukan cewa ana fama da matukar karancin kudi a bankuna, na’urorin ATM da POS har zuwa wajen 'yan canji.

Jawabin da ya fito daga bankin CBN

"Hankalin CBN ya kai ga rahotanni cewa ana fama da karancin kudi a bankuna, ATM, PoS da BDC a wasu manyan biranen kasar nan.
Bincikenmu ya nuna karancin kudin da ake samu a wasu wurare a sanadiyyar yawan cire kudi da bankuna su ka yi ne daga CBN.
Sannan kuma mutane sun rude sun yi ta cire kudi daga na’urar ATM. - CBN

Bankin ya ce yadda aka rika gigin cire kudi daga bankuna ne ya jawo karancin takardun Nairori da ake ta kokawa a yanzu.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kungiyar CAN ta yi martani game da harin bam kan masu Maulidi a Kaduna, ta tura bukata

Kamar yadda babban bankin ya sanar, akwai isassun kudin da ake bukata, Naira ba tayi karanci kamar yadda wasu ke tunani ba.

Masu POS sun ce babu kudi

Legit tayi magana da wani mai aikin POS a Samaru-Zariya wanda ya shaida mata cewa N20, 000 kadai ake iya samu daga bankuna.

"N20, 000 kurum ake ba mu idan ka bi layi a banki, kuma mutum daya kadai zai ce yana son duka N20, 000 din a shagonka."

- Mai POS a Samaru

An nemi ECOWAS ta gaggauta cire takunkumi

Ana da labari tsohon gwamnan CBN, Muhammadu Sanusi II ya bukaci shugabannin ECOWAS su janye takunkumin da ke kan Nijar

Khalifan darikar Tijjaniyan kasar ya ce suna fata da rokon Allah a daga takunkumin da aka daura kan kasar Nijar tun watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel