Juyin Mulki: ECOWAS Ta Dauki Muhimmin Mataki Domin Dawo da Mulkin Farar Hula a Nijar
- Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS ta kafa wani kwamiti da zai dawo da tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar
- Kwamitin ya ƙunshi shugabannin ƙasashen Togo, Saliyo da Jamhuriyar Benin, domin tattaunawa da gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar
- An bayyana hakan ne a wajen taro na 64 na shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS da aka yi a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta dauki muhimmin mataki na dawo da tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.
Ƙungiyar ECOWAS, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta kafa kwamitin shugabannin ƙasashe da za su tattauna da CMSP, gwamnatin mulkin sojan Nijar.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me nene amfanin kwamitin?
Ngelale ya ce an kafa kwamitin ne a ƙarshen taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS karo na 64 a Abuja.
A cewar sanarwar, ƙungiyar ECOWAS ta yi alƙawarin sassauta takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar a hankali bisa sakamakon da aka cimma a tattaunawar.
Shugabannin ƙasashen na Yammacin Afirika sun jaddada cewa a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar Mohammed Bazoum da ake tsare da shi ba tare da wani sharaɗi ba.
Wacce buƙata ECOWAS ke nema a wajen CMSP?
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Hukumar ta yi matukar takaicin cigaba da tsare Shugaba Mohammed Bazoum da iyalansa da muƙarrabansa da gwamnatin CMSP ke yi."
“Hukumar ta kuma nuna rashin jin daɗin ta game da rashin ƙoƙarin CMSP na dawo da tsarin mulki, saboda haka hukumar ta yi kira ga CMSP da ta saki Shugaba Mohammed Bazoum, da iyalansa, da kuma muƙarrabansa cikin gaggawa ba tare da wani sharaɗi ba."
Akwai lauje cikin nadi: Atiku ya ki sakin bayanan takardun karatunsa bayan ya fallasa Shugaba Tinubu
"Bisa sakamakon yarjejeniyar da kwamitin shugabannin ƙasashen da CMSP suka cimma, hukumar za ta cigaba da sassauta takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar."
"Idan CMSP ta gaza yin aiki da sakamakon da aka cimma da kwamitin, ECOWAS za ta bar dukkanin takunkumin da aka ƙaƙaba mata, ciki har da yin amfani da ƙarfi, sannan ta buƙaci ƙungiyar tarayyar Afirika da sauran abokan hulda da su aiwatar da takunkumin da aka sanya wa mambobin CMSP da muƙarrabansu."
Sanusi Lamido Ya Shawarci ECOWAS
A wani labarin kuma, Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II ya buƙaci ƙungiyar ECOWAS ta cire takunkumin da ta ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar.
Sanusi II ya bayar da wannan shawarar ne a taron da ya halarta na shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng