Ministan Tinubu Ya Tono Adadin Bashin Titunan da Shugaba Buhari Ya Tafi Ya Bari

Ministan Tinubu Ya Tono Adadin Bashin Titunan da Shugaba Buhari Ya Tafi Ya Bari

  • David Umahi zai sake yin nazari a game da bashin ayyukan da ‘yan kwangila su ke bin gwamnatin tarayya
  • Ministan ayyukan tarayya ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta bar masa gadon bashin Naira tiriliyan 1.5
  • Sanata Umahi ya nada wasu kwamitoci na musamman da za su yi aiki a duka bangarori shida da ke kasar nan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta ce an kafa wani kwamiti da zai duba bashin da ke tsakanin ‘yan kwangila da gwamnatin Najeriya.

Rahoto ya fito daga The Nation cewa ‘yan kwangilan da ke yi wa ma’aikatar ayyuka ta kasa aiki su na bin gwamnatin tarayya bashin N1.5tr.

Ministan Tinubu - Buhari
Tsohon shugaban kasa da Ministan ayyuka, David Umahi Hoto: Muhammadu Buhari/Dave Umahi
Asali: Facebook

Minista ya kafa kwamitoci 6

Kara karanta wannan

An kawo wata dabarar tsige Gwamnan PDP, Magoya bayan Minista ba su hakura ba

Ministan ayyukan tarayya, Sanata David Umahi ya fitar da jawabi cewa kwamitoci shida aka kafa su yi aiki a kowane yanki da ke kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitocin za su duba takardun aiki kafin Mayun 2023 da kuma ayyukan bayan 29 ga watan Mayu 2023 da Bola Tinubu ya hau kan mulki.

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin Sakataren yada labaran Ministan, Orji Uchenna Orji.

Orji Uchenna Orji ya ce kwamitocin za su sake duba sabanin farashin da aka samu kan kwangilolin da aka amince da wadanda ba a amince ba.

A karshe kwamitocin za su ba Mai girma Minista da ma’aikatar shawarwarin da za a dauka.

Umahi ya ce Buhari ya bar bashin N1.5tr

A cewar Ministan, bashin da ya gada daga hannun gwamnatin baya ya haura Naira tiriliyan guda a sakamakon tashin farashin kaya a kasar.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki yayin da gwamnatin Tinubu ke sharholiya - Rahoto

Daily Trust ta ce hauhawar farashin da kaya su ke yi a kasuwa ya yi tasiri a kwangilolin, hakan zai kara yawan talakawa a Najeriya.

David Umahi wanda ya godewa Bola Tinubu kan yadda ya ba shi goyon baya domin ganin an gyara tituna, ya ce lamarin ya fi karfin kasafin kudi.

Tinubu bai tanka Mambila ba

Ana da labari ma'aikatar wuta za ta kashe miliyoyi wajen zuwa taro a kasar waje, amma babu kudin aikin lantarkin Mambilla a shekarar 2024.

Ganin yadda aka tsara kasafin kudin na badi, kungiyar NEF ta Dattawan Arewa ta ce gwamnatin Bola Tinubu ba ta san abin da yake yi mata ciwo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng