Innalillahi: Rayukan Mutum 16 Sun Salwanta, Wasu Mutum 27 Sun Jikkata a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Innalillahi: Rayukan Mutum 16 Sun Salwanta, Wasu Mutum 27 Sun Jikkata a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin hanyar Abuja zuwa Kaduna ya salwantar da rayukan mutum 16
  • Wasu mutum 27 kuma sun samu raunuka a hatsarin da ya ritsa da wata babbar motar ɗaukar kaya ƙirar DAF
  • Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa wacce ta tabbatar da aukuwar hatsarin ta ce mutanen da suka jikkata an kai su asibiti

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kaduna ta ce aƙalla mutum 16 ne suka mutu sannan wasu 27 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamandan shiyyar, Mista Kabir Nadabo, ya ce hatsarin motan ya auku ne a ƙauuyen Audu Jhangon da ke kan titin ranar Abuja zuwa Kaduna a Lahadi, 10 ga watan Disamba, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da ramin hakar ma'adanai ya rufta kan mutane a jihar Arewa

Mutum 16 a hatsarin mota a Kaduna
Rayukan mutim 16 sun salwanta a kan titin hanyar Abuja zuwa Kaduna Hoto: FRSC Nigeria
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:20 na safe, inda wata mota ƙirar DAF mai lamba KUJ 430XC ɗauke da kaya masu yawa, ta ƙwace ta faɗa cikin rami, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin ya auku

"Rahotanni na farko sun nuna direban na cikin tsananin gudu, wataƙila saboda gajiya ta ƙwace masa. Tawagar masu aikin ceto na RS1.114 Zhipe da RS1.16B Dutse ne suka gudanar da aikin ceton." A cewarsa.
"Hatsarin ya ritsa da mutane 65, inda 27 suka jikkata, sannan mutane 16 suka rasu. An kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin yi musu magani."

Nadabo ya ce da samun labarin aukuwar hatsarin, ya ziyarci wurin domin samun bayanai na gani da ido tare da jagorantar tawagar masu aikin ceto wajen kwashe waɗanda suka rasu zuwa ƙakin ajiye gawarwaki.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin masu maulidi yan bindiga sun halaka mutum 33 a wani sabon hari

"Na kuma umurci motar ɗaukar kaya da ta cire wani ɓangare na tirelar da ya tare wani ɓangare na hanyar. Ana ci gaba da gudanar da aikin, kuma titin za a iya wucewa kansa." A cewarsa.

Mutum 5 Sun Rasu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu mutum 11 a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Calabar zuwa Itu a jihar Akwa Ibom.

Hatsarin ya ritsa da wata mota ƙirar Nissan Caravan mai lamba GWB532XY da wata babbar mota ƙirar Mark wacce ba ta da lamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng