Gwamnan Katsina Ya Dakatar da Shugaban Makarantar Sakandire Kan Abu 1

Gwamnan Katsina Ya Dakatar da Shugaban Makarantar Sakandire Kan Abu 1

  • Gwamnan jihar Katsina ya dakatar da wani shugaban makarantar sakandiren gwamnati a ƙaramar hukumar Dandume
  • Gwamnan ya dakatar da shugaban makarantar ne bisa zarginsa da cin zarafin wata ɗaliba ta makarantarsa
  • A umarnin da gwamnan ya bayar, ya buƙaci a gudanar da bincike kan lamarin tare da miƙa masa rahoto

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jiihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin dakatar da wani shugaban makarantar sakandare bisa zargin yin lalata da wata ɗaliba.

Gwamnatin dai ta dakatar da shugaban makarantar sakandiren gwamnati da ke Dantankari a ƙaramar hukumar Dandume a jihar.

Gwamna Radda ya dakatar da shugaban makarantar sakandire
Gwamna Dikko Radda ya dakatar da shugaban makarantar sakandire Hoto: Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Meyasa Gwamna Radda ya dakatar da shugaban makarantar?

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Aliyu Yar’adua ta ce gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayar da umarnin dakatar da Lawal Ibrahim nan take bisa zargin cin zarafin ɗalibar.

Kara karanta wannan

Magidanci ya yi kokarin salwantar da ran matarsa kan abu 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin bincike kan zarge-zargen tare da miƙa masa rahoto bayan an kammala.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Gwamna ya samu rahoto kan zargin cin zarafi a kan wani Lawal Ibrahim (ma’aikacin ma’aikatar ilimi) wanda a lokacin shi ne shugaban makarantar sakandiren gwamnati ta Dantankari da ke ƙaramar hukumar Dandume a kan zargin lalata da wata ɗalibar makaranta."
A sakamakon haka, Gwamnan ya bada umarni kamar haka, kwamishinan Ilimi ya gaggauta dakatar da Lawal Ibrahim tare da bincike kan zargin, ɗaukar matakin da ya dace, sannan a kai rahoto ga gwamna."

An umarci ƴan sanda su gudanar da bincike

Ya kuma buƙaci kwamishinan ƴan sandan da ya binciki zargin.

"An umarci kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina ya yi bincike kan zargin sannan ya binciki DPO na Dandume bisa zargin haɗa baki da shi kan lamarin." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya bayyana yankin da zai amfana da mulkin Shugaba Tinubu

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya ce rundunar ta san da wannan zargi, kuma tuni ta fara bincike kan lamarin.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗan jihar Katsina mai suna Umar Idris wanda ya koka kan yadda ake ƙara samun taɓarɓarewar tarbiyya a makarantu.

A kalamansa:

"Abubuwa ne waɗanda ba yanzu suka fara ba, saboda yadda tarbiyya ta yi ƙaranci tsakanin malamai da ɗalibai. Akwai ƙarancin tsawatarwa tsakanin malamai da ɗalibai."
Abun Allah wadai ne irin waɗannan abubuwan da ke faruwa sannan ya kamata gwamnati ta sanya ido sosai da sanya dokoki masu tsauri kan malaman da ke ƙulla wata alaƙa da ɗalibai wacce ba koyo da koyarwa ba."
"Ya kamata gwamnati ta ɗauki hukunci mai tsauri kan duk wanda aka samu da irin wannan ta yadda zai zama darasi ga duk masu shirin yi a nan gaba."

Mataimakin Shugaba Ya Yi Wa Daliba Ciki

Kara karanta wannan

Kujerun Ciyamomi 31 sun fara tangal-tangal a ranar da gwamnan PDP ya rantsar da su

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke wani mataimakin shugaban makarantar sakandire bisa zargin yi wa wata ɗaliba ciki.

An dai kama Malam Ibrahim ne bayan ɗalibar da ya yi wa ciki, mai shekaru goma sha biyu, ta haihu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng