Asiri ya tonu: An kama shugaban makaranta da yake iskanci da wasu daliban shi tagwaye

Asiri ya tonu: An kama shugaban makaranta da yake iskanci da wasu daliban shi tagwaye

- Wani shugaban makarantar sakandire a jihar Legas mai suna Samson Adeyemo ya shiga hannun 'yan sanda

- Ana zargin shi da laifin lalata da wasu tagwaye masu kananan shekaru a makarantar har da dura wa daya daga cikinsu juna biyu

- Amma Adeyemo yace ya auri Hassanar ne kuma iyayenta sun sani, ita kuwa Hussainar kishi take yi da son mijin 'yar uwarta

Wani shugaban makarantar sakandire a jihar Legas mai suna Samson Adeyemo, ya bayyana dangantakar da ke tsakanin shi da wasu tagwaye biyu a makarantar da yake shugabanta.

Adeyemo mai shekaru 41 na zama ne a lamba 8 titin Odesanya kuma shine shugaban kwalejin Legati dake Abule Egba.

Ana zargin shi da laifuka biyu ne da suka hada da lalata da yara.

A rahoton da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya gani a ranar Litinin daga wajen dan sanda mai kara, M.I. Oshodi, wanda ake zargin na da shaidar dufuloma ne ta malinta kuma ana zargin shi da lalata kananan yaran tagwaye.

"Ina da alaka da tagwayen amma na auri Hassanar ne. Ba a yi auren a coci ba ko kotu amma iyayen sun sani. Aure ne tsakanina da Hassanar kuma iyayenta sun sani. Mun fara alaka da Hassanar ne a 2016 amma sai 2017 na kwanta da ita. Ban fara komai da Hussainar ba har sai da na hadu da mahaifiyarsu."

Adeyemo ya tabbatar da cewa makarantar da yake shugabanta a jihar Legas bata da rijista da ma'aikatar ilimin jihar.

KU KARANTA: Ganduje zai hana aurar da yara mata har sai sun kammala makarantar sakandare

Amma kuma ya musanta alakar jima'i da sauran daliban. Wanda ake zargin ya tabbatar da cewa Hassana na da cikin kuma yana kula da ita. An fara rigimar kishi ne bayan da Hussaina ta gano yana da alaka da Hassanarta.

Adeyemo yayi wa Hassanar ciki amma iyayen sun jaddada cewa sai dai a zubar. Bayan kudin kula da kanta da ya bata, sun zubar da cikin.

Amma bayan kwanaki kadan sai suka bukaci N200,000 ko kuma ya fuskanci fushin hukuma. Malamin bai kai ga bada kudin ba sai kawun tagwayen ya same shi inda yayi mishi duka kuma ya mika shi ga 'yan sanda.

Wannan laifin yaci karo da sashi na 137 na Criminal Law na jihar Legas na 2015. Jastis Sherifat Solebo ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel