Katsina: An cafke mataimakin shugaban makarantar sakandire saboda yi wa daliba ciki
- Mataimakin shugaban makarantar sakandire a karamar hukumar Rimi ya shiga hannun jami'an tsaro
- An kama Malamin mai suna Ibrahim bisa zarginsa da dirkawa daya daga cikin dalibansa ciki
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke Malam Ibrahim Tukur, mataimakin shugaban makarantar sakandire a karamar hukumar Rimi bisa zarginsa da yi wa daya daga cikin dalibansa ciki.
An kama Malam Ibrahim ne bayan dalibar da ya yi wa ciki, mai shekaru goma sha biyu, ta haihu, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
A ranar Laraba ne rundunar 'yan sanda ta yi holin masu kaifuka daban-daban, cikinsu har da Malam Ibrahim.
Ana tuhumar dukkan mutanen da laifi mai nasaba da fyade kuma sun shiga hannun ne a tsakanin ranar 9 zuwa ranar 14 ga watan Janairu, 2021.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya shaidawa manema labarai cewa sun kama mataimakin shugaban makarantar ne ranar 9 ga watan Janairu bayan shigar da korafi akansa a ofishin 'yan sanda na Rimi.
A cewar rundunar 'yan sanda, wani mutum ne mai suna Ibrahim Sani ya shigar da korafi akan Malam Ibrahim a ofishin 'yan sanda.
SP Isah ya bayyana cewa Malam Ibrahim ya yi amfani da matsayinsa wajen yaudarar yarinyar tare da yi mata ciki.
KARANTA: Korona ta hallaka daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria, ya rasu ya bar Rolls Roys 10
"Mataimakin shugaban makarantar yana da mata uku, amma a hakan ya ke daukan yarinyar zuwa gidansa tare da kwanciya da ita. A haka ciki ya shiga har ya girma, daga karshe sai tiyata aka yi aka fitar da jariri," a cewarsa.
Daga cikin mutanen da aka yi bajakolinsu akwai Auwal Hamzat da Sulaiman Abubakar wadanda ake zargi da lalata wasu yara maza guda uku.
Makwabta ne suka fara shigar da korafi a ofishin rundunar 'yan sanda har ta kai ga an kama masu laifin.
Legit.ng ta rawaito cewa a ranar Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa rundunar jami'an tsaro ta 'Thunder Srike' ta kaddamar da harin kwanton bauna akan wasu 'yan bindiga a yankin karamar hukumar Kagarko.
Mista Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, ya sanar da cewa jami'an tsaro sun kashe biyu daga cikin 'yan bindigar a cikin jawabin da ya fitar.
A cewar Aruwan, rundunar jami'an tsaro ta samu nasarar kaddamar da harin ne a daren ranar Litinin a kan hanyar Sabon Iche zuwa Kagarko.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng