Yan Najeriya Na Fama da Matsin Tattalin Arziki Yayin da Gwamnatin Tinubu Ke Sharholiya – Rahoto

Yan Najeriya Na Fama da Matsin Tattalin Arziki Yayin da Gwamnatin Tinubu Ke Sharholiya – Rahoto

  • A yayin da 'yan Najeriya ke fama da rayuwa kan matsin tattalin arziki da kasar ke ciki, an gano hanyoyin da gwamnati ke batar da kudin kasar
  • Tun daga zuwa taruka a kasashen duniya, zuwa tafiye-tafiye da sayen motocin alfarma, gwamnatin Tinubu ta kashe makudan kudade a hawanta mulki
  • Da yawa daga 'yan Najeriya sun yi korafi kan "almubazzaranci da dukiyar kasa" da gwamnati ke yi ta fuskar sharholiya, alhalin rayuwa na kara tsada a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Halin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki ya tilasta 'yan kasar daukar matakan rayuwa a ciki, da yawa daga tsare-tsaren gwamnatin kasar na samun suka daga jama'a.

Kara karanta wannan

Zo ka nemi aiki: Dan Najeriya ya nemo kamfanin da ke biyan albashin naira miliyan 3 duk wata

Jaridar Vanguard ta fara nazarin mukarraban gwamnati da Shugaba Tinubu ya nada, da kuma shirinsa na yin garambawul a hukumomi, ma'aikatu da bangarori na gwamnati.

An zargi gwamnatin Tinubu da sharholiya
A yayin da 'yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki, wani rahoto ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke sharholiya da kudaden kasar. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tun daga shekarar 1999 ba a taba samun gwamnati mai tarin mukarrabai irin ta Tinubu ba, ko ministoci akwai 48 yanzu a kasar, kamar yadda Majalisar Tarayya ta tantance su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina kudin kasar ke tsirarewa?

Otel din UNGA: A watan satumba, gwamnati ta kashe naira miliyan 390.7 kan dakunan kwanan wakilan data tura taron majalisar dinkin duniya (UNGA) a birnin New York, rahoton Vanguard.

Sakataren fadar shugaban kasa, Adebiyi O. Olufunso ya sanar da hakan a ranar 11 ga watan Satumba, inda masu fashin baki ke ganin kudaden sun yi yawa, musamman a halin matsin tattali da kasar ke fama da shi.

Taron COP28 a Dubai: Najeriya ta kashe makudan kudade wajen tura wakilai karon dumamar yanayi a Dubai. Duk da an rawaito wakilai 1,411 ta tuwa, gwamnatin kasar ta ce mutum 422 kawai ta dauki nauyin su.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa: Take-taken Tinubu sun nuna bai damu da gyara tsaron Arewa ba

Sharholiya a kasafin kudin 2023

Jirgin ruwan alfarma na shugaban kasa: A watan Nuwamba, aka ware naira biliyan 5.1 don siya wa shugaban kasa jirgin ruwa na alfarma.

Duk da cewa rahoto ya nuna tun a zamanin mai girma Buhari aka amince a sayi jirgin, sai dai majalisar tarayya ta dau aniyar karkatar da kudin zuwa asusun tallafa wa daliba.

An ware wa kowanne dan majalisar tarayya naira miliyan 160 don sayen manyan motocin alfarma, ban da makudan kudi na alawus da ake ba su.

Sai kuma a hannu daya, gidan zaman mataimakin shugaban kasa a Abuja ya lakume naira biliyan 20.5 wajen gyara, haka aka ware naira biliyan 3 don gyara gidan shi na Legas.

Sharholiya a kasafin kudin 2024

Kasafin 2024: A kasafin kudin 2024 kuwa, 'yan Najeriya sun yi korafi kan yadda aka ware naira biliyan 319.28 don watsa labarai, walwala da kiwon lafiya a fadar shugaban kasa da wasu bangarori na gwamnati.

Kara karanta wannan

"Ban ji dadi ba": Tinubu ya magantu kan kisan masu maulidi a Kaduna, ya bayar da wani umurni

An kuma ware naira biliyan 61.29 don gyare-gyare da gine-gine; sai kuma tafiye-tafiyen shugaba Tinubu da mataimakinsa zuwa kasar waje zai lakume naira biliyan 7.5.

Fannin abinci a ma'aikatun Gwamnatin Tarayya kuwa ya samu naira biliyan 5.84 yayin da fadar shugaban kasa ta samu naira biliyan 6.2 don hawan motoci.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da muhimmancin kasafin 2024 na kawo babban ci gaba a tattalin arziki da gina Najeriya, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Yan Arewa sun fusata

A wani labarin kuma, sannan kasafin kudin 2024 ya fusata 'yan Arewa, domin babu abin da aka ware domin ayi aikin kwangilar wutan lantarkin Mambilla da ke garin Gembu a jihar Taraba a shekarar 2024.

Kungiyar manyan Arewa ta NEF ta zargi gwamnatin Bola Tinubu da watsi da Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.