Kotu Ta Daure Matashi Wata 6 a Gidan Kaso Saboda Satar Maggi da Sabulu, Alkali Ya Ba Shi Zabi

Kotu Ta Daure Matashi Wata 6 a Gidan Kaso Saboda Satar Maggi da Sabulu, Alkali Ya Ba Shi Zabi

  • Dubun wani matashi ya cika bayan kama shi da zargin satar katon din Maggi da kuma sabulun wanka a Jos da ke jihar Plateau
  • Wanda ake zargin mai suna Jemilu Bala dan shekaru 22 ya tabbatar da aikata laifin da ake tuhumarsa a kai inda ya nemi sassauci
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a, Shawomi Bokkos ya daure shi a gidan gyaran hali har na tsawon watanni shida da zabin biyan tara dubu 20

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Kotun yanki da ke zamanta a Jos a jihar Plateau ta yanke wa wani matashi watanni shida a gidan gyaran hali kan zargin satar sabulu.

Wanda ake zargin mai suna Jemilu Bala dan shekaru 22 ya kuma saci katon din Maggi wanda jimillar kudin ya kai naira dubu 55.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame lebura wata 7 a gidan gyaran hali kan satar agwagi guda 3 a Filato

Kotu ta daure matashi watanni shida kan zargin satar Maggi
Dubun matashi ya cika bayan kama shi da zargin satar Maggi da sabulu. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke kan matashin a Plateau?

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Shawomi Bokkos ya daure matashin bayan ya amince da aikata laifin inda ya bukaci sassauci daga kotun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun ya kuma bai wa matashin zabin biyan tara na naira dubu 20, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Ibrahim Gokwat ya bayyana cewa sun samu rahoton satar ce a ranar 10 ga watan Oktobar wannan shekara.

Yaushe aka kama matashin da zargin satar a Plateau?

Dan sandan ya ce Mista Gbenga Ayantola ne ya kawo rahoton satar a ofishin 'yan sanda na yankin 'A' a ranar, cewar Osun Reporters.

Ya ce wanda ake zargin ya tsallaka zuwa shagon ajiye kaya inda ya saci katon din Maggi da kuma sabulu da kudinsu ya kai dubu 55.

Kara karanta wannan

Yanzu: An nemi ministan tsaron Tinubu ya yi murabus kan kisan masu Maulidi a Kaduna

Ya kara da cewa yayin binciken 'yan sanda wanda ake zargin ya amsa dukkan abin da ake tuhumarsa a kai.

Kotu ta garkame matashi kan zargin kisan kawunsa

A wani labarin, kotu ta garkame wani matashi kan zargin kisan kawunsa saboda zargin maita a jihar Adamawa.

Wanda ake zargin, John Clackson ya hallaka kawunsa mai suna Mohammed Clackson a karamar hukumar Guyuk a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.