EFCC da DSS Sun Yi Yunkurin Garkuwa da Emefiele Daga Gidan Yarin Kuje? Hukumar NCS Ta Yi Martani
- Hukumar Gidajen Yari a Najeriya (NCS), ta yi martani kan jita-jitar sace tsohon gwamna CBN, Godwin Emefiele da ke tsare a hannunsu
- Hukumar ta ce wannan labarin kanzon kurege ne wanda ba shi da tushe bare makama yayin da ta tabbatar da cewa ya na tare da su
- Wannan na zuwa ne bayan zargin jami’an DSS da EFCC sun yi yunkurin yin garkuwa da Emefiele karfi da yaji daga gidan yarin Kuje
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kwanturolan Hukumar Gidan Yari (NCS), Haliru Nababa ya yi martani kan jita-jitar cewa an yi yunkurin yin garkuwa da Godwin Emefiele.
Nababa ya ce babu kamshin gaskiya a cikin labarin na cewa hukumar EFCC da DSS su na kokarin yin garkuwa da tsohon gwamnan CBN, Legit ta tattaro.
Mene ake yada wa kan Emefiele?
An yi ta yada cewa EFCC da DSS sun yi yunkurin ne don dauke Emefiele da karfi daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta tattaro cewa an gano wasu jami’an EFCC sun zagaye gidan yarin a kokarin dauke Emefiele.
Nababa ya fayyace haka ne yayin da amsa gayyatar Majalisar Wakilai a jiya Alhamis 7 ga watan Disamba.
Mene martanin NCS kan Emefiele?
Wannan na zuwa ne bayan Hukumar kare hakkin dan Adam da kuma adalci ta zargi DSS da EFCC bayan sun yi kokarin dauke tsohon gwamnan CBN.
New Telegraph ta tattaro Nababa na cewa:
“Kamar yadda ake ciki yanzu, ba mu da wani bayani kan yunkurin dauke Emefiele da karfi, har yanzu ya na tare da mu.”
Kwanturolan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa mai kula da bangaren ayyuka, Nwakeze Emmanuel ya bukaci mutane su yi watsi da jita-jitar.
Kotu ta ba da belin Emefiele
A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele kan zargin badakalar kudade.
Wannan na zuwa bayan an zargi tsohon gwamnan da almundahana da kudade yayin da ya ke bankin a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng