Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele

  • Godwin Emefiele wanda ke fuskantar tuhume-tuhume a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, zai cigaba da zama a gidan gyaran hali
  • Tsohon gwamnan na CBN zai cigaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan belinsa na N300m
  • Kotun ta kuma ɗage sauraron shari'ar har sai zuwa ranar 18 ga watan Janairu domin cigaba da sauraron ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya kasa cika sharuɗɗan belinsa.

Emefiele zai ci gaba da zama a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da ya cika sharuɗɗan belinsa na biyan N300m.

Emefiele zai cigaba da zama a gidan gyaran hali
Godwin Emefiele ya kasa cika sharuddan belinsa Hoto: @thecableindex
Asali: UGC

Kamar yadda gidan talabijin na TVC ya ruwaito, kotun ta dage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2024 domin cigaba da shari'ar.

Kara karanta wannan

Sarki ya raba wa mutanensa tukunyar girki na gas, ya yi gargadi su daina amfani da itace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta bayar da belin Emefiele

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya samu beli bayan babbar kotun tarayya da ke Maitama a birnin tarayya Abuja ta amince da buƙatarsa ta neman beli.

Kotun ta bada belin tsohon gwamnan na CBN kan kuɗi Naira miliyan 300 da kuma kawo mutum biyu waɗanda za su tsaya masa waɗanda ke da shaidar mallakar kadarori a Maitama cikin birnin Abuja.

Haka kuma kotun ta wajabta wa Mista Emefiele ya miƙa dukkanin takardunsa na tafiye-tafiye ga rijistaran kotun kuma ko an sake shi a beli dole ya zauna a yankin ƙaramar hukumar Abuja Municipal.

Kotu ta tura Emefiele gidan gyaran hali

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja a Maitama, ta umurci a tsare tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gidan gyaran hali na Kuje kafin ya cika ƙa'idar belinsa.

Mai Shari'a Hamza ne ya bada umurnin a ranar Juma'a bayan gurfanar da Emefiele tare da musanta aikata laifuka shida da Hukumar EFCC ke tuhumarsa a karar da ta yi wa kwaskwarima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel