Lokacin da Ake Jira Ya Zo, Dangote Ya Fara Shiryen Shiryen Tace Danyen Man Farko
- NNPCL zai ba kamfanin Dangote danyen man da zai fara tacewa bayan kammala gina matatarsa a Legas
- An dauko mai da za a kai matatar da aka yi shekaru ana aikinta, za a fara samun fetur da dizil a cikin gida
- Za a dauki shekaru kusan biyu kafin aiki ya kankama sosai ta yadda za a iya tace ganguna 400,000 a rana
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Lagos - Bayan dogon lokaci da je-ka-ka-dawo, matatar man Aliko Dangote da ta ci kusan $20bn za ta fara aiki a Najeriya.
Leadership ta ce za a fara tace mai a katafariyar matatar domin kamfanin zai karbi danyen mai da aka shigo da shi daga waje.
Wata majiyar S&P Global ta shaida cewa motar kaya ta OTIS dauke da ganguna 950, 000 na tulin danyen mai ta na kan hanya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna ana sa ran motar za ta isa unguwar Lekki da ke Legas a makon nan, daga nan za a karasa zuwa matatar.
Rahoton S & P ya nuna Najeriya da ke ji da kan ta a matsayin babba a Afrika za ta samu damar tace mai yanzu a cikin gida.
NNPCL zai ba Dangote danyen mai
NNPCL wanda ya saye 20% na hannun jarin matatar Dangote ta yarda a ba kamfanin gangunan danyen mai miliyan shida.
This Day ta nuna matatar za ta samu danyen mai ne aga rijiyar Agbami wanda yake karkashin kulawar kamfanin Chevron.
Yadda Dangote zai samu mai
Ana samun ganguna 100, 000 duk rana daga rijiyar da ke Neja-Delta, sai zuwa 2025 matatar za ta rika tace ganguna 370, 000.
Masana sun ce man ya shahara saboda sinadarin sulphur 0.04% da yake da shi kuma ana yawan samun naphtha da kananziri.
Kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya shiga yarjejeniya domin ya rika ba Dangote danyen man da zai tace a sabuwar matatar.
Matatar za ta rika tace danyen mai iri uku: Escravos, Bonny Light da Forcados da za su rika bada fetur, dizil, kananzir da kuma LPG.
Dangote ya yi fama da matsala
Duk da ana ikirarin an gama gina matatar man tun watan Mayu, ba a iya fara aiki ba har zuwa yanzu saboda wasu dalilai da-dama.
An dauki dogon lokaci kafin a tsara yadda za a ba kamfanin attajirin 'dan kasuwan mai saboda yarjejeniya da wasu kamfanoni.
Asali: Legit.ng