‘Yan Majalisan da Aka Yi a 1992 Sun Tuno da Tsohon Bashin da Su ke Bin Gwamnati
- Tsofaffin ‘yan majalisar wakilai sun tuna da cewa akwai wasu hakkokin da su ke bin gwamnatin tarayya
- ‘Yan siyasar sun roki gwamnatin Bola Tinubu ta biya su albashi da alawus na aikin da su ka yi a 1992-1993
- Sani Abacha ya raba su da aikinsu da ya ruguza majalisar tarayya bayan yi wa Ernest Shonekan juyin mulki
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Wasu ‘yan siyasan da su ka wakilci mazabunsu a majalisar wakilan tarayya a 1992 sun kai kuka wajen gwamnatin Najeriya.
Premium Times ta ce tsofaffin ‘yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya ta biya su wasu hakkokinsu da su ka ce sun makale.
Rayuwa ta juyawa tsofaffin 'yan majalisa baya
Wadannan Bayin Allah da su ka rike kujerar majalisar wakilai daga 1992 zuwa 1993 sun kira taron manema labarai ne a garin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da Ibrahim Badamasi Babangida yake mulki, an zabi mutane 593 da su ka zama ‘yan majalisa, daga baya aka yi juyin mulki.
A sakamakon juyin mulkin da Sani Abacha ya yi wa Cif Ernest Shonekan, gwamnatin soja ta cire mutane su ka zaba a SDP da NRC.
Wahalar tsofaffin 'yan majalisa a yau
Hon. Amina Aliyu ta yi jawabi a wajen taron ‘yan jaridan da aka kira ranar Laraba, ta ce tsofaffin abokan aikinsu sun tagayyara a yau.
Vanguard ta ce tsohuwar ‘yar majalisa ta yi bayanin yadda takwarorinta ke fuskantar matsalolin rashin lafiya da kalubale na rayuwa.
Wani tsohon ‘dan majalisa ya yi kira ga Bola Tinubu wanda ya yi Sanata a lokacin, ya biya su alawus da albashin da su ke bin gwamnati.
'Yan majalisa sun biyo bashin albashi?
A cewar Hon. Basil Okafor, suna bin gwamnati bashin albashin lokacin da su ka yi aiki.
‘Yan siyasar su ka ce wasunsu sun mutu a halin yanzu, wadanda ke raye kuwa ba sui ya tabuka komai don haka dole su ke neman agaji.
Fred Agbedi wanda ‘dan majalisa ne mai-ci da ya wakilci mazabarsa a 1992, ya biye masu wajen neman a biya wadannan hakkoki a yau.
Kasafin kudin 2024 a Majalisa
A baya an samu labari cewa Yusuf Shitu Galambi ya ce Shugaban kasa ya gabatar da kundin kasafin kudi ba tare da cikakken bayani ba.
Daga baya an samu wadanda su ka yi wa Hon Yusuf Galambi raddi, su ka ce Bola Tinubu ya kawo kundin ne a cikin na'urar komfuta.
Asali: Legit.ng