A Wata Daya: ’Yan Sanda Sun Damke Masu Laifi 130 a Katsina, Sun Gurfanar da 61

A Wata Daya: ’Yan Sanda Sun Damke Masu Laifi 130 a Katsina, Sun Gurfanar da 61

  • Rundunar 'yan sanda ta sanar da nasarar da dakarunta suka samu na afke masu laifi 130 a jihar Katsina
  • A cikin wata daya rundunar ta samu wannan nasarar kamar yadda kakakin rundunar na Katsina ya bayyana
  • Daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan fashi 38, masu kisan kai 16, da sauransu, kuma ta kubutar da mutum 69

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce ta samu nasarar cafke mutane 130 da ake zarginsu da laifukan ta'addanci a watan Nuwamba 2023.

Rundunar ta yi nuni da cewa cikin manyan laifukan ta'addanci 81 da ta yi aiki kansu, an gurfanar da 61 gaban kotu don yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Ku zo ku siya: An saka jirgin shugaban Najeriya a kasuwa, ana neman mai saye

Rundunar 'yan sanda/Jihar Katsina
A cikin manyan laifukan ta'addanci 81 da rundunar 'yan sanda ta yi aiki kansu a wata daya, ta gurfanar da mutum 61 gaban kotu don yanke hukunci. Hoto: Nigerian Police
Asali: Facebook

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarorin da rundunar ta samu a wata daya

Zantawar ta shafi irin nasarorin da rundunar ta samu a cikin wata daya kan yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda, rahoton Leadership.

Ya ce:

"A cikin wata daya, mun samu ayyukan ta'addanci tamatin da daya kamar su fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai, satar shanu da sauransu.
"Mun kama wadanda ake zargi mutum 130 inda tuni muka gabatar da mutum 63 gaban kotu don yanke masu hukunci."

Rundunar ta kakkabe masu garkuwa da mutane

Kakakin rundunar ya ce mutum 38 an kama su da laifin fashi da makami, mutum 16 kuma laifin kisan kai.

Rundunar ta kuma kama wani mai laifi da kwayoyi, yayin da ta kama wasu 42 da laifuka daban daban da suka hada da barazana, tayar da tarzoma, daba da sauransu.

Kara karanta wannan

Maulidi: Atiku ya yi martani kan harin bam da aka yi kan bayin Allah a Kaduna, ya ba da shawara

Aliyu ya kuma kara da cewa rundunar ta samu nasarar kubutar da mutum 69 da aka yi garkuwa da su, tare da kakkabe masu garkuwa uku, da kwato makamai da harsasai.

KatsinaHukumar yan sandan NAjeriyaYan ta'addaYaki da ta'addanci a Najeriya​

A wani labarin, mahaifiyar rikakken dan daba a jihar Kano, ta yi ta-maza inda ta mika shi ga 'yan sandan jihar, Legit Hausa ta ruwaito.

A baya ne rundunar 'yan sanda ta sanya kyautar naira dubu dari biyar ga duk wanda ya gano inda dan dabar mai suna Hantar Daba ya ke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.