Katsina: An damke wasu ‘yan fashi da makami bayan layan da suka dogara a kai ta yake musu hanzari

Katsina: An damke wasu ‘yan fashi da makami bayan layan da suka dogara a kai ta yake musu hanzari

- Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wasu ‘yan fashi da makami

- ‘Yan fashi da makamin sun yi amfani da laya don kare kansu, amma layan ta ki aiki a lokacin

- Kwamishinan ‘yan sanda ya ce za’a gurfanar da wadanda ake tuhuma a kotu bayan kammala bincike

Akalla 'yan fashi da makami biyar ne jami'ai na ‘yan sandan jihar Katsina suka cafke, bayan layan da suka dogara a kai don kare su ta yake musu hanzari .

Legit.ng ta tattaro cewa wadanda ake tuhuma sun yi amfani da laya don kare kansu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Besen Gwana, wanda ya bayyana hakan yayin da ake nuna wadanda ake zargi tare da wasu wadanda aka kama saboda laifuffuka daban-daban a jihar.

Katsina: An damke wasu ‘yan fashi da makami bayan laya da suka dogara ta yake musu hanzari

'Yan fashi da makami

Wadanda ake zargin sun hada da; Usman Lawal Dawa, mai shekaru 30 da haihuwa daga Kamfanin Doka, Birnin Gwari, jihar Kaduna da Umaru Audu Sunaya Soja (mai shekaru 30) da Ibrahim Abubakar (mai shekaru 37) da Bashir Ahmadu (mai shekaru 39) da kuma Gambo Musa wanda aka fi sani da suna ‘Killer’, (mai shekaru 28) kuma dukanin su daga kauyen Tashar Bawa da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

KU KARANTA: An kashe mutane 10 a wani harin da aka kai a Kaduna

CP Gwana ya ce an kama wadanda ake tuhuma a wani yankin karamar hukumar Sabuwa na jihar a ranar 6 ga watan Janairu bayan wani bayanan sirri.

CP ya ci gaba da cewa an samu wadannan ‘yan fashi da kudi dalar Amurka guda 10 na $100 wanda ake zargi cewa jabu ne.

Sauran abubuwa da aka samu daga ‘yan fashin sun hada da bindigogi kerar gida da harsasai da kuma waya tarho guda bakwai wanda ake zargi kayan sata ne.

Kwamishinan ‘yan sanda ya ce za’a gurfanar da wadanda ake tuhuma a kotu bayan kammala bincike.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel