Jerin Lokutan da Sojoji Suka Yi Kuskuren Jefa Bama-Bamai Kan Fararen Hula a Najeriya
An sha samun kuskuren kai hare-haren bam a kan fararen hula da ba su san hawa ba su san sauka ba a Najeriya.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Haren-haren waɗanda ake kuskuren kai wa kan fararen hula dai, ƴan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya aka nufa da su.

Asali: Getty Images
Tun daga shekarar 2017 dakarun sojojin Najeriya, sun yi kuskuren kai hare-haren bam kan fararen hula har sau shida, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Ga jerin lokutan a nan ƙasa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin Rann
A ranar 17 ga watan Janairun 2017, sama da mutum 52 ne suka mutu sannan 120 suka jikkata a wani harin bam da aka kai a sansanin ƴan gudun hijira da ke garin Rann na jihar Borno.

Kara karanta wannan
Kaduna: Rundunar Sojin Ƙasa ta ɗauki laifi, ta faɗi gaskiyar abinda ya jawo jefa bam a taron Maulidi
Harin Damboa a Borno
A ranar 13 ga watan Afrilun 2020, wani jirgin yaƙin sojojin saman Najeriya ya kai harin bam a ƙauyen Sakotoku da ke ƙaramar hukumar Damboa a jihar Borno, inda ya kashe fararen hula 17 da suka haɗa da mata da ƙananan yara.
Harin Kurebe
A cikin watan Afrilun 2022, jirgin sojojin saman Najeriya ya kashe yara shida a ƙauyen Kurebe da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Bama-baman dai an harbo su ne kan ƴan ta'addan da ke yin sintiri a yankin.
Harin Kunkuna
A ranar 7 ga watan Yulin 2022, wani jirgin yakin sojin saman Najeriya ya kai harin bam a ƙauyen Kunkuna da ke ƙaramar hukumar Safana ta Katsina inda ya kashe mutum 13 da suka haɗa da mata da ƙananan yara.
Harin Doma
A cikin watan Janairun 2023, wasu bama-bamai da jiragen yakin sojin saman Najeriya suka harba, sun kashe mutum 37.

Kara karanta wannan
Jerin haɗurran jiragen Rundunar Sojin Najeriya 4 da suka auku a 2023 tare da dalilai
Harin dai ya auku ne a kan iyakar jihohin Benue da Nasarawa a ƙaramar hukumar Doma ta jihar Nasarawa, inda ya ritsa da mutane ciki har da Makiyaya.
Harin Tudun Biri
A ranar 3 ga watan Disamban 2023, jirgin sojojin Najeriya mara matuƙi ya kashe mutum 85 a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna, cewar rahoton Trust Radio.
Ahmed Guni Ya Ɗauki Zafi Kan Kisan Tudun Biri
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannan malamin addinin musuluncin nan Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana kan harin da sojoji suka yi kuskuren kai wa kan fararen hula a ƙauyen Tudun Biri.
Sheikh Gumi ya yi tir da harin wanda ya halaka fararen hula masu yawa, inda ya bayyana cewa wannan wani lamari ne da ke faruwa a Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng