Rundunar Sojin Najeriya Ta Kare Matakin Kai Harin Bam Kan Masu Maulidi, Ta Fadi Dalilanta

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kare Matakin Kai Harin Bam Kan Masu Maulidi, Ta Fadi Dalilanta

  • Sojojin Najeriya sun kare matakin kai harin bam a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna kan masu Maulidi
  • Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri ne kan gungun 'yan ta'adda a yankin wanda su ke shirya kai harin ta'addanci a yankin
  • Ta shawarci jama'a da su na ba da rahoton irin wadannan taruka don bai wa rundunar damar tantance na banza da na kirki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Rundunar sojin Najeriya ta kare matakin kai harin bam a wani kauye da ke jihar Kaduna.

A ranar Lahadi ce 3 ga watan Disamba ce rundunar sojin ta sake bam a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi da ke jihar.

Kara karanta wannan

"Ban ji dadi ba": Tinubu ya magantu kan kisan masu maulidi a Kaduna, ya bayar da wani umurni

Sojojin Najeriya sun kare matakin kai harin bam a Kaduna
Sojoji a Najeriya sun yi martani kan harin bam a Kaduna. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Mene rundunar ta ce kan harin?

Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba shi ya tabbatar da haka a yau Talata 5 ga watan Disamba, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edward ya ce rundunar ta kai harin ne bayan samun bayanan sirri cewa akwai 'yan ta'adda a yankin Ligarma da misalin karfe 10 na dare.

Ya ce jirgin sama ya gano musu wasu gungu da su ke zargin 'yan ta'adda ne ganin yadda su ie lamuransu irin na 'yan ta'adda.

Ya kara da cewa dandazon 'yan ta'adda da su ka gani barazana ce ga fararen hula wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba, cewar Leadership.

Buba ya ce sun dauki matakin ne don dakile barazanar kai hari ga mazauna yankunan.

Wace shawara rundunar ta bayar?

Sanarwar ta ce:

"Ya kamata ku sani 'yan ta'adda na shiga cikin jama'a don kai hari ga al'umma.

Kara karanta wannan

Yan sanda za su fara kama duk wanda ba a san tushen arzikinsa ba

"Duk da haka, rundunar soji na iya kokarinta don bambance jama'a da kuma sauran 'yan ta'adda.
"Rundunar a kullum ta na ganin mutuwar farar hula a matsayin abin takaici wanda dole a kiyaye shi."

Kakakin rundunar ya ce dole jama'a su kiyaye taro irin wannan ba tare da sanar jami'an tsaro ba wanda hakan zai ba su damar tantance na kirki da na banza.

Ya ce mafi yawan 'yan ta'addan na amfani da taron jama'a don gudanar da ayyukan ta'addanci musamman a yankunan da ake fama da hare-haren 'yan bindiga.

Rundunar sojin sama ta wanke kanta kan harin bam

A wani labarin, Rundunar sojin saman Nigeriya ta yi martani game da harin bam kan ma su Maulidi a jihar Kaduna.

Wannan na zuwa bayan hallaka wasu masu bikin Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.