Ba Za Ta Yiwu Ba: Sojoji Sun Fusata Pantami Da Hadimin Buhari Da Kisan Masu Maulidi

Ba Za Ta Yiwu Ba: Sojoji Sun Fusata Pantami Da Hadimin Buhari Da Kisan Masu Maulidi

  • Sojojin Najeriya sun ce an yi kuskure wajen harba bam da ya yi sanadiyyar mutane da ke taron mauludi a garin Kaduna
  • Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce wajibi ne a gudanar da bincike na musamman domin a iya hukunta masu laifin
  • Bashir Ahmaad ya soki aikin dakarun sojojin, yake cewa dole a tabbatar da hakan ba za ta sake faruwa a wani wuri nan gaba ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Sojojin Najeriya sun hallaka wasu Bayin Allah da ke Maulidi a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a karshen makon jiya.

Wannan abin da dakarun sojojin kasar su ka kira kuskure ya batawa al’umma rai, ganin adadin mutanen da aka rasa daga kuskuren.

Kara karanta wannan

Ba yau ne farau ba: Kwankwaso ya yi tir da Sojojin da su ka kashe mutane a Kaduna

Jirgin sojoji
Jirgin sojoji ya kashe 'yan maulidi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jama'a sun soki 'kuskuren' sojoji a Kaduna

Tsohon Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami ya na cikin wadanda su ka yi Allah wadai da abin da ya faru a shafin sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da ya yi magana a dandalin Twitter, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna akwai bukatar ayi bincike domin a dauki mataki a kai.

"Kusan mutane 150 da ba su yi laifin komai ba, daga ciki akwai mata, yara da sauransu sojojin gwamnatin tarayya su ka harbawa bam su ka mutu a Kaduna yau.
Mu na ta’aziyya ga dangoginsu. Dole a hukunta wadanda su ka yi wannan domin rashin adalci a ko ina, barazana ne ga adalci."

- Isa Ali Pantami

Mutane sun goyi bayan kiran da malamin addinin musuluncin ya yi ganin kuskuren sojojin ya kashe Bayin Allah a Zamfara da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

Bashir Ahmad wanda ya yi aiki da Muhammadu Buhari a matsayin Mai taimakawa a kafofin sadarwa na zamani, ya na tare da Isa Pantami.

"Haba! Ba za ku kashe rayuka 126 ba su ji ba, ba su gani ba – mutum 126 masu fararen kaya, kuma ku kira shi kuskure ba.
Ba zan ma iya tuna lokacin da dakarun sojoji su ka hallaka ‘yan ta’addan da adadinsu ya kai haka a duk fadin kasar nan ba.
‘Yan Najeriya na jiran @HQNigerianArmy domin jin yadda za a gyara ‘kuskuren’ da matakan da aka dauka domin hana aukuwarsa."

- Bashir Ahmaad

Sojoji su ka kashe 'Yan maulidi?

Daga baya an samu labari cewa Gwamnatin Kaduna ta bayyana gaskiyar yadda aka yi har sojoji suka jefa bam kan masu bikin Maulidi a Igabi.

Karin hasken ya zama dole ne bayan sojojin sama sun nesanta kan su daga zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng