Yayin farautar yan bindiga, Sojoji sun kashe mana daruruwan Shanu: Fulani a Nasarawa
- Shugabannin Fulani sun bayyana yanda harin ya kasance a Ranakun Alhamis da lahadi
- Kimanin shanu Dari biyar ne suka tarwatse aka rasa inda suke
- Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa kimanin shanu Dari ne suka mutu a harin
- An kaddamar da hare-haren ne tsakanin ranakun Alhamis da Lahadi
Jiragen Sojoji biyu sun hallaka sama da Shanu 1000 a hare-haren da suka kai garuruwan Fulani a kananan hukumomin Keana da Doma na jihar Nasarawa.
Shugabannin Fulani da wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa an fara kai hare-haren ne tsakanin ranar Alhamis, 10 ga Yuni da Lahadi, 13 ga Yuni.
Wasu matasan Fulani makiyaya da ke kula da shanun sun samu raunuka yayin da ba a gano shanu sama da 500 da suka watsu zuwa makwabtan jihar Binuwai, in ji wadanda lamarin ya rutsa da su.
Wasu majiyoyi sun ce an kashe daruruwan shanu a yankin Giza na Karamar Hukumar Keana a kan dalilin cewa sojoji na aiki don fatattakar ‘yan fashi daga yankunan.
An bayyana cewa aikin daya gudana a ranar Lahadi ya dauki tsawon awanni uku kuma ya haifar da tashin hankali a yankunan yayin da manoma da Fulani makiyaya suka kaurace wa gidajensu saboda tsoron kada a kashe su.
"Jirgin da ya gudanar da aikin yana karkashin jagorancin Operation Whirl Stroke na sansanin Sojin saman Najeriya da ke Makurdi a Jihar Benuwe," in ji wata majiya.
"Wasu‘ yan bindiga ne suka harbi jirgin saman soja; wannan shi ne abin da ya haifar da ruwan bama-bamai ga dukkanin yankin. Daya daga cikin bindigogin an zana shi da launukan Sojojin Sama na Najeriya yayin da dayan kuma aka zana shi da launin koren sojoji. ”
Sai dai wasu shugabannin Fulanin sun ce harin ya farune ba tare da wata tsokana ba.
Shugaban riko na kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a jihar Nasarawa, Bala Mohammed Dabo, ya ce an kuma kashe daruruwan shanu tsakanin Kwatanbala da Akwanaja a karamar hukumar Doma.
A wani hari na daban a ranar Alhamis a Kuduku na karamar hukumar Keana, Alhaji Jigawa ya rasa shanu da yawa yayin mamayar.
Asali: Legit.ng