Rundunar Sojin Sama Ta Yi Martani Kan Zargin Kai Harin Bam Kan Masu Maulidi a Kaduna, Ta Roki Jama'a

Rundunar Sojin Sama Ta Yi Martani Kan Zargin Kai Harin Bam Kan Masu Maulidi a Kaduna, Ta Roki Jama'a

  • Yayin da ake cikin tashin hankali na harin bam kan masu Maulidi, rundunar sojin sama ta yi martani kan lamarin
  • Rundunar ta karyata labarin da ake yadawa inda ta ce babu kamshin gaskiya a ciki, ta kuma bukaci ayi watsi da labarin
  • Martani rundunar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar, Edward Gabkwet ya fitar a yau Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Rundunar sojin saman Nigeriya ta yi martani kan jita-jitar cewa jirginta ya babbake wasu masu taron Maulidi a jihar Kaduna.

Rundunar ta ce wannan labarin kanzon kurege ne babu inda su ka harba bam cikin kuskure kan masu Maulidin.

Kara karanta wannan

Kaduna: Rundunar Sojin Ƙasa ta ɗauki laifi, ta faɗi gaskiyar abinda ya jawo jefa bam a taron Maulidi

Sojin sama sun yi martani game da harin bam kan masu bikin Maulidi a Kaduna
Rundunar sojin sama ta musanta zargin kai harin kan masu Maulidi. Hoto: Nigerian Airforce.
Asali: Getty Images

Mene ake zargin sojin saman?

Rahotanni sun ruwaito cewa jirgin saman ya jefo bam kan masu Maulidin a zaton ko 'yan ta'adda ne, Legit ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martani rundunar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar, Edward Gabkwet ya fitar a yau Litinin 4 ga watan Disamba.

Sanarwar ta ce:

"Ya kamata a sani cewa rundunarmu ba ta kai wani hari ba a cikin sa'o'i 24, kuma ba rundunarmu kadai ba ce ke da jirgi maras matuki a yankin Arewa maso Yamma.
"Ya kamata gidajen yada labarai su rinka tantance rahoto da kuma sanin tushen shi kafin yadawa, mun gode."

Wane martani rundunar ta yi kan harin na bam?

Wannan na zuwa ne bayan samun rahotanni cewa sojojin saman Najeriya sun jefo bam kan masu bikin Maulidi a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari'ar zaben dan Majalisar PDP, ta bayyana mai nasara

Daga bisani, rundunar sojin kasa sun yi martani inda su ka tabbatar da cewa su ne su ka kai harin amma a bisa kuskure ba da niyya ba.

Sojoji sun harba bam kan masu Maulidi a Kaduna

A wani labarin, A yau an waye gari da mummunan labari inda harin bam ya kashe wasu masu bikin Maulidi a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a kauyen Tudun Biri da ke akramar hukumar Igabi da ke jihar wanda ya yi ajalin mutane fiye da 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.