Watanni da Hana Shi Minista El-Rufai Ya Yi Watsi da Siyasa Ya Bude Kamfani a Abuja
- Kamfanin Afri-Venture Capital Company Ltd zai fara aiki a farkon shekarar 2024 a birnin tarayya Abuja
- Nasir El-Rufai ya sanar da haka a dandalin Twitter, ya ce suna fatan kamfanin zai taimakawa al’umma
- Mutanen tsohon gwamnan irinsu Jimi Lawal, Hafiz Bayero, Eyo Ekpo da Kabir Yabo za su rike kamfanin
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bayan shekaru takwas ya na gwamna a jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun kafa kamfanin da zai taimakawa tattalin arziki.
Malam Nasir El-Rufai ya sanar da wannan a shafinsana Twitter a safiyar ranar Litinin.
Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa kamfaninsu mai suna Afri-Venture Capital Company Ltd zai fara aiki a Junairun shekarar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin Afri-Venture Capital Company Ltd
Tsohon gwamnan yake cewa Jimi Lawal, Hafiz Bayero, Eyo Ekpo da kuma Kabir Yabo za su zama Darektocin da su ka kafa kamfanin.
Shi kuma Nasir El-Rufai zai zama shugaban da ke kula da ayyukan kamfanin, yana mai neman addu’ar mutane domin a fara aiki a sa’a.
‘Dan siyasar ya kuma bukaci jama’a su taya su da addu’a wajen ganin masu kirkire a Najeriya da na kasashen Afrika sun yi zarra a duniya.
Malam El-Rufai wanda ya koma yin karatun PhD a kasar waje yake cewa suna fata za su zama tamkar kamfanin Dangote a nan gaba.
Wani aiki El-Rufai za su yi a Afri-Venture Capital Company Ltd?
Business Day ta rahoto cewa kamfanin Afri-Venture Capital Company Ltd zai soma da jarin $100m domin ya taimakawa masu tasowa.
Da alama Afri-Venture Capital Company Ltd zai maida hankali ne ga masu harkar fasahar zamani musamman a Kaduna da kewayen jihar.
Nasir El-Rufai ya kawo $2m
Kamar yadda yaronsa, Bashir El-Rufai ya shaida, tsohon Ministan na Abuja zai $2m daga cikin dukiyarsa domin ganin kamfanin ya mike.
Malam Bashir El-Rufai ya ce dalilin yin hakan shi ne saboda masu hannun jari su gamsu, su shigo ayi wannan tafiya da su a kamfanin.
El-Rufai wanda aka yi tunanin zai zama Minista ya fara shaidawa duniya wannan ne a wajen wani taro da aka yi Marrakech a Moroko.
Wa ya hana Nasir El-Rufai zama Minista?
Ana kawo Nasir El-Rufai a cikin 'yan siyasan da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi niyyar zai ba mukami, daga baya aka canza shawara.
An zargi Kashim Shettima, Godswill Akpabio, Femi Gbajabiamila da Nuhu Ribadu da hannu wajen yakar Nasir El-Rufai a gwamnati mai-ci.
Asali: Legit.ng