Waye Zai Yi Nasara a Kotu? Jigon Siyasa Ya Hango Abin da Zai Faru a Shari’ar Abba da Gawuna
- Jigon APC ya bayyana hasashensa game da hukuncin kotun koli kan karar da Gwamna Abba Yusuf da Caleb Mutfwang suka kai
- Mista Williams Dakwom, ya bayyana kwarin gwiwarsa ga bangaren shari’a, yana mai cewa hukuncin kotun koli ba zai bambanta da hukuncin kotun daukaka kara ba
- Hakan na zuwa ne bayan da dan takarar jam’iyyar APC, Nasir Gawuna ya yi nasara a kotun daukaka kara
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Filato - Kotun Koli za ta yanke hukunci kan karar da Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da Caleb Mutfwang na jihar Filato suka shigar, inda suke kalubalantar hukuncin kotunan zabe da kuma hukuncin kotun daukaka kara.
A baya an kori gwamnonin biyu tare da ba abokan hamayyarsu gaskiya duba da wasu hujjojin da aka gabatar a gaban alkalai.
Mista Williams Dakwom, mamban majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a jihar Filato, ya ce kotun koli ba za ta yi watsi da kotun daukaka kara da kuma hukuncin kotun zabe da ya soke zaben Mutfwang da Yusuf ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun koli za ta duba hukuncin baya
Jigon jam'iyyar ya jaddada mahimmancin kiyaye ka'idojin tsarin mulki tare da bayyana imaninsa ga tsarin doka cewa, na iya magance matsalolin da suka faru kafin zabe da kuma bayan zabe.
A wata tattaunawa ta musamman da wakilin Legit a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, 2023, Dakwom ya bayyana cewa, APC ta fuskanci irin wannan yanayi a 2019 a Zamfara, inda suka rasa mukamai sakamakon wasu kura-kuran da aka samu a taron gangamin jam’iyyar.
Don haka Dakwom ya nuna yadda jam’iyyar ta amince da shan kaye da kuma bin ka’idojin dimokradiyya da dokar kasar nan.
Abubuwan da za a yi duba gare su
Saboda haka yace, hukuncin kotun koli da ake jira zai yi daidai da abin da kotunan baya suka yanke game da makomar Abba da Mutfwang.
A kalamansa:
"Kotun koli za ta duba hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a jihohi daban-daban, shin kotun daukaka kara ta bi ka'ida ko kuwa?
“Idan kuma suka gano akwai wata doka da ta goyi bayan hakan, kuma wadannan mutanen ba su bi doka ba, don haka dole su karbi abin da zai biyo baya.”
An yi hukunci tsakanin Abba da Doguwa
A wani labarin, babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin Gwamna Abba Kabir a Kano kan zargin Alhassan Doguwa da ta'addanci.
Kotun ta yi watsi da karar inda gwamnan ke zargin dan Majalisar Tarayya, Alhassan Ado Doguwa da hannu a kisan kai a lokacin zabe.
Asali: Legit.ng