Shari'ar Gwamnan Kano da Sauran Hukunce-Hukuncen Kotun Daukaka Kara 3 Da Suka Jawo Cece-Kuce
Ƴan Najeriya da dama sun yi zargin kotun ɗaukaka ƙara ta yin tufka da warwara a hukuncin da alƙalanta suka yanke a wasu ƙararrakin zaɓe.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ƴan Najeriyan dai na zargin cewa kotun na yi wa dokar zaɓe fassara fiye da ɗaya wajen zartar da hukunci a shari'a iri ɗaya.
Ga huɗu daga cikin hukunce-hukuncen da kotun ɗaukaka ƙara ta zartar waɗanda suka janyo cece-kuce:
Shari'ar zaɓen gwamnan Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP a ranar 20 ga watan Satumba, inda ta ba ɗan takarar APC Nasiru Yusuf Gawuna nasara.
Kotun ta kuma yi hukunci cewa ba ta da hurumin yanke hukunci kan ƙorafin APC na halascin zaman Gwamna Abba ɗan takarar NNPP, inda ta ce wannan batu ne na kafin zaɓe.
Ko da Gwamna Abba ya garzaya zuwa kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja sai ta yi hukunci cewa kotun zaɓe na da hurumin sauraron batun halastaccin takarar Abba.
Kotun ta kuma yi hukunci cewa gwamnan ba halastaccen ɗan takarar NNPP ba ne, saboda babu sunansa a rajistar mambobin jam’iyyar da ta ba hukumar zaɓe ta INEC kafinzaɓe.
Saboda haka ita ma kotun sai ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano na ranar 18 ga watan Maris 2023.
Shari'ar zaɓen gwamnan Plateau
Gwamna Caleb Mutfwang ya yi nasara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Plateau, inda ta yi watsi da ƙalubalantar nasararsa a zaɓe kan rashin shugabancin jami’iyya da kuma saɓa dokar zaɓe da ɗan takarar APC, Nentaye Goshwe Yilwatsa ya yi.
Sai dai, bayan Nentawe ya ɗaukaka ƙara a kotun ɗaukaka ƙara, kotun ta soke hukuncin kotun zaɓen inda ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Kotun ta tsige Gwamna Mutfwang ne bisa dogaro da sashe na 177 na kundin tsarin mulki, kan cewa jam'iyyarsa ba ta gabatar da shi a matsayin ɗan takararta bisa tsari ba, kuma ta saba umarnin kotu na gudanar da zaben shugabanni a ƙananan hukumomi 17 na jihar.
Kotun ta kuma bayyana cewa batun halascin tsayawa takara ya shafi gabanin zaɓe da kuma bayan zaɓe, inda tace haka kotun zaɓe ta yi kuskure kan cewa ɗan takarar na APC ba ya da hurumin ƙalubalantar tsayawa takarar Mutfwang.
Shari'ar zaɓen gwamnan Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC ya yi rashin nasara a kotun sauraron ƙararrakin gwamnan jihar Nasarawa, inda kotun ta bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Kotun ta bayyana cewa ba a tsayar da Abdullahi Sule takara ta halastacciyar hanya ba, domin ba ya cikin waɗanda suka shiga zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar da uwar jam’iyyar APC ta gudanar.
Sai dai, gwamnan ya yi nasara da ya ɗaukaka ƙara a kotun ɗaukaka ƙara inda ta soke hukuncin kotun zaɓen tare da tabbatar da nasararsa a zaɓen.
Shari'ar zaɓen gwamnan Zamfara
Kotun ɗaukaka ƙara a shari'ar zaɓen gwamnan jihar Zamfara ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba a shari'ar da Bello Matawalle ya ɗaukaka.
Kotun ta kuma ba hukumar zaɓe ta INEC umarnin ta sake zaɓe a ƙananan hukumomi uku da suka haɗa da Maradun, Bukkuyum da Birnin Magaji
Kotun ta bayyana cewa INEC ta yi kuskure bisa dogara da bayanan da ke shafinta na IReV na tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar, saboda haka ta soke nasarar Gwamna Dauda Lawal Dare na Jami’iyyar PDP a zaɓen.
Gwamnonin PDP da Suka Yi Nasara a Kotu
A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnoni ta tabbatar da nasarar wasu gwamnoni na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023.
Kotun ta tabbatar da nasararsu ne bayan ƴan adawa sun ƙalubalanci nasararsu a kotu. Gwamna Bala Mohammed da Caleb Mutfwang na daga cikin waɗanda suka yi nasara.
Asali: Legit.ng