Sarakunan Najeriya 3 Sun Mutu a Mummunan Hatsarin Mota
- Mummunan hatsarin mota ya yi ajalin wasu sarakunan gargajiya uku a yankin Oriire da ke jihar Oyo
- An rahoto cewa biyu daga cikin sarakunan sun mutu nan take yayin da cikon na uku ya rasu a asibiti
- Sarakunan da suka rasu sun hada da OLODOGBO na Odogbo, Onibowula na Bowula da Alayetoro na Ayetoro a karamar hukumar Oriire
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Mazauna karamar hukumar Oriire da ke jihar Oyo suna cikin halin juyayi sakamakon mutuwar sarakunan yankin uku a daren ranar Juma'a.
Sarakunan sun mutu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da motar Benz E230 dauke da lambar OLODOGBO da wata babbar motar kasuwa mai lamba 301 XF a Aje Iye da ke karamar hukumar Oriire, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Twitter
Biyu daga cikin sarakunan sun mutu nan take wajen da abun ya faru yayin da na ukun ya mutu yan awanni a tsakani a asibitin koyarwa na jami'ar Ladoke Akintola inda yake jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarakuna 3 sun rasu a hanyar zuwa taro
Fasinjoji shida ne hatsarin ya ritsa da su amma uku da suka rayu suna jinya a asibitin koyarwa na LAUTECH.
Za su halarci wani taro ne a garin da ke makwabtaka lokacin da hatsarin ya afku.
Sarakunan da abun ya ritsa da su sune OLODOGBO na Odogbo, Onibowula na Bowula da Alayetoro na Ayetoro a karamar hukumar Oriire.
Da yake tabbatar da lamarin, kwamandan hukumar FRSC na yankin, Joshua Adekanye, ya ce karo na gaba da gaba motocin biyu suka yi hanyar babban titin Ogbomoso-Oyo.
Ya ce wadanda suka rayu suna jinya a asibitin koyarwa na LAUTECH, yayin da akan kwashi gawawwakin mamatan zuwa sashin ajiye gawa na asibitin.

Kara karanta wannan
"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa
Fasinjoji 13 sun jikkata a hatsarin mota
A wani lamari makamancin wannan, Adekanye ya ce tara daga cikin fasinjoji 13 sun ji raunuka daban-daban lokacin da motar DAF ta kama wuta a hanyar titin Ogbomoso-Oyo a wannan rana, rahoton Punch.
Ya kara da cewar ba a rasa rai ba amma wadanda suka jikkata na samun kulawa a asibitin.
Hatsarin tirela ya lakume rayuka 17
A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa wani mummunan hatsarin motar tirela ya yi ajalin mutane akalla 17 tare da jikkata wasu a jihar Neja.
Hatsarin ya afku ne a kauyen Takalafiya da ke karamar hukumar Magama da ke jihar, Punch ta tattaro.
Asali: Legit.ng